An fara aikin gina sabon titin jirgin ƙasa na zamani daga Legas zuwa Ibadan

An fara aikin gina sabon titin jirgin ƙasa na zamani daga Legas zuwa Ibadan

- Aikin gina titin jirgin kasa daga jihar Legas zuwa Ibadan ya fara gadan gadan

- Hukumar kula da jiragen kasa ta kasa ta fara rusa gine ginen dake kan hanyoyin jiragen kasa

Cikin shirye shiryen fara gudanar da aikin shimfida layin dogo irin na zamani daga garin Legas zuwa Ibadan, hukumar kula da layin dogo na kasa, NRC, ta fara yin rusau akan gine gine da suka shiga layin dogon.

NRC ta fara gudanar da aikin rusau din ne a unguwannin Apapa, hanyar Legas zuwa Ijoko, da kuma wani sashi na jihar Ogun.

KU KARANTA: Ma’aikata sun jefi gwamnan jihar Kogi akan rashin biyan albashi

Babban manajan NRC, Injiniya Fidet Okhiria ya bayyana cewa a ranar Alhamis 14 ga watan Afrilu ne za’a fara aikin shimfida layin dogon, wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar.

An fara aikin gina sabon titin jirgin ƙasa na zamani daga Legas zuwa Ibadan

Sabon jirgin ƙasa na zamani

Shi dai wannan aikin kamar yadda NAIJ.com ta samu bayanai, shahararren kamfanin gine gine na kasar Sin, CCECC ne ke gudanar da aikin gina shi, kuma aikin wani bangare ne na aikin gina titin jirgin kasa daga Legas zuwa Kano.

Dayake yi ma manema labaru jawabi, daraktan NRC yace ya zama lallai su rushe duk wani gini dake kan hanyarsu, saboda zai yi amfani anan gaba.

An fara aikin gina sabon titin jirgin ƙasa na zamani daga Legas zuwa Ibadan

Ranar da Osinbajo ya kaddamar da aikin sabon titin jirgin ƙasa na zamani daga Legas zuwa Ibadan

“Da gangan muka ki baiwa duk wasu masu gine gine a wurin nan daman gini saboda mun san wata rana za’a bukaci amfani da filin. Don haka mun riga mun ware wuraren da zamu rushe, kuma mun sanar dasu.” Inji Darakta Okhiria.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya kaddamar da aikin layin dogo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel