YANZU YANZU: An bayyana ‘yar jigon PDP Tony Anenih a matsayin mamallakiyar gidan da EFCC suka gano makudan kudi

YANZU YANZU: An bayyana ‘yar jigon PDP Tony Anenih a matsayin mamallakiyar gidan da EFCC suka gano makudan kudi

- Rahotanni ya kawo cewa ginin da hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta gano makudan kudi mallakar ‘yar babban jigon PDP ne

- A cewar rahotan gidan mallakin tsohon gwamnan jihar Bauchi ne amma sashin da aka gano kudin na ‘yar Tony Anenih ne

Rahotanni dake zuwa ya nuna cewa ginin da hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta gano dala miliyan 43 ($43 million), naira miliyan 23 (N23 million), fam 27,800 (£27,800) a unguwar Ikoyi dake jihar Lagas a ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu mallakar ‘yar babban jigon PDP ne.

A cewar Sahara Reporters, yanzu an tabbatar da cewa wannan ginin da ake magana a kai mallakar wata ‘yar tsohon shugaban kungiyar amintattu na jam’iyyar PDP Tony Anenih ne.

A bayanin ta, kafar watsa labaran ta yanar gizo, wacce da farko ta ruwaito cewa mallakar tsohon shugaban PDP Adamu Mua’azu ne, tace tsohon gwamnan jihar Bauchi ne keda gidan, amma wannan sashi mallakar ‘yar Anenih ne.

YANZU YANZU: An bayyana ‘yar jigon PDP Tony Anenih a matsayin mamallakiyar gidan da EFCC suka gano makudan kudi

An bayyana ‘yar jigon PDP Tony Anenih a matsayin mamallakiyar gidan da EFCC suka gano makudan kudi

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta kuma babban kamu a jihar Lagas (HOTO)

Ta buga a shafin ta na twitter a ranar, 13 ga watan Afrilu:

NAIJ.com ta tuna cewa da farko Sahara Reporters ta ruwaito cewa an yi zargin cewa kudin na tsohuwar manajan darakta na kamfanin NNPC Esther Nnamdi-Ogbue ne.

A bangaren ta, hukumar EFCC ta ce bazata iya tabbatar da wanda ya mallaki kudin ba har sai ta gama gudanar da binciken ta.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wani mutumi da ya nemi a yi shara a majalisar dattawan Najeriya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel