Magu bai bukatan majalisan dattawa ta tabbatar da shi

Magu bai bukatan majalisan dattawa ta tabbatar da shi

- Osinbajo yayi fashin baki akan rashin tabbatar da Ibrahim Magu

- Yace babu wanda ya isa yay a hana Magu aiki kuma ba za’a cire shi ba

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yayi fashin baki akan zancen Shugaban hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, Ibrahim Magu, inda yace bai bukatan su tabbatar da shi.

Osinbajo wanda yayi magana da manema labarai wanda aka shirya a fadar Shugaban kasa ya kawo hujja cewa sashe na 1, sakin layi na 71 na kundin tsarin mulkin Najeriya. Wannan hujja be cewa majalisan dattawa ba tada hurumin tabbatar da Magu kafin ya cigaba da aiki.

Magu bai bukatan majalisan dattawa ta tabbatar da shi - VP Osinbajo

Magu bai bukatan majalisan dattawa ta tabbatar da shi - VP Osinbajo

A maimakon bata lokaci Jan cewa majalisan dattawa ta tabbatar da Magu, mataimakin Shugaban kasa yace kamata yayi majalisan dokokin tarayya ta taimaka wajen karfafa kotunan Najeriya saboda su daina bata lokaci wajen hukunci.

KU KARANTA: Rundunar soji ta hallaka yan Boko Haram da dama

Yace dalilin da ya sa fadar Shugaban kasa ta ki bin umurnin kotu wajen sakin shugaban Yan Shia , Ibrahim Zakzaky , da tsohon NSA Sambo Dasuki, saboda lauyoyi masu bata lokaci wajen yanke hukunci.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel