Hukumar EFCC ta rufe gidaje da kadarorin tsohon gwamnan PDP a Arewa

Hukumar EFCC ta rufe gidaje da kadarorin tsohon gwamnan PDP a Arewa

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta rufe gida da kadarorin tsohon gwamnan Neja Dakta Mu'azu Babangida Aliyu

- Kadarorin na a kan titin Peter Sarki Tunga a Minna a yammacin jiya

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta rufe gida da kadarorin tsohon gwamnan Neja Dakta Mu'azu Babangida Aliyu dake kan titin Peter Sarki Tunga a Minna a yammacin jiya.

Mai karatu da zai iya tuna cewa mun ruwato cewa Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC), ta kama tsohon gwamnan jihar Neja Dr Mu'azu Babangida Aliyu kan zargin cin hanci da rashawa da halatta kudaden haram.

NAIJ.com ta samu labarin cewa mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa da majiyar mu cewa hukumar tana rike da tsohon gwamnan.

Hukumar EFCC ta rufe gidaje da kadarorin tsohon Gwamnan PDP a Arewa

Hukumar EFCC ta rufe gidaje da kadarorin tsohon Gwamnan PDP a Arewa

"Yana hannunmu kuma muna cigaba da yi masa tambayoyi," in ji mista Uwujaren.

Sai dai bai yi karin haske kan abin da ake tuhumur tsohon gwamnan da aikata wa ba.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta sake gano wasu makudan kudade

Hakazalika bai bayyana lokacin da hukumar za ta gurfanar da Dr Aliyu a gaban kotu ba.

Tsohon gwamnan na Neja ya shafe shekara takwas yana mulkin jihar daga shekarar 2007 zuwa ta 2015.

Kuma ya fadi takarar kujerar majalisar dattawa da ya nema a zaben 2015.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

ku kalli yadda wasu jami'an gwamnati suke a kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel