Gaskiya na kan bayyana! Ga abin da tsohon Shugaban PDP na cewa game da kudi miliyan $50 da EFCC suka gano a Ikoyi (HOTUNA)

Gaskiya na kan bayyana! Ga abin da tsohon Shugaban PDP na cewa game da kudi miliyan $50 da EFCC suka gano a Ikoyi (HOTUNA)

- Mallam Muazu ya kira dandalin ‘Sahara’ jim kadan bayan da aka buga rahoton

- No 16 Osborne Towers, Ikoyi , Legas, inda EFCC suka gano miliyan $50 tsabar kudi

- Muazu bai mallaki wani gida a Ikoyi, fãce gidansa a Walter Carrington, Victoria Island Legas

- Mr Oyegoke ya ce maigidansa bai ji dadi game da labarin da aka buga

- Wanda suke kusa da tsohon shugaban PDP sun tabbatar da cewa shi ne mai dukiya

Tsohon shugaban jami’yyar PDP, Adamu Mu'azu ya ƙaryata game da gidan inda jami’an hukumar laifufukan tattalin EFCC a ranar Laraba 12 ga watan Afrilu suka gano fiye da miliyan $50 da aka boye a bayan ganuwar na karya hasumiyan gida a yankin masu kudi a Ikoyi Legas.

Mallam Muazu ya kira dandalin ‘Sahara’ jim kadan bayan da aka buga rahoton duk da haka, ya kasa bayyana dalilin da kamfani da ya gina gidan ya jera sunansa a matsayin abokin ciniki.

KU KARANTA: Malabu: Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya shiga uku

NAIJ.com ya tara rahoto cewa, Etco Nigeria Limited, wani masu shiri gini da wani kamfani Isra'ila Electrical Limited, sun mallaki rabi, suna alfa’ari a matsayin wadanda suka gina gidaje da dama na zama da kuma kamfanoni a Abuja, da kuma Legas har da dukiya a No 16 Osborne Towers, Ikoyi , Legas, inda EFCC suka gano miliyan $50 tsabar kudi da aka tusa kabad da wuta ba ta ci bayan wani bangon ƙarya a ranar Laraba da sakan rana.

Wanda suke kusa da tsohon ciyaman na PDP sun tabbatar da cewa Muazu yake da gida da EFCC suka gano miliyan $50

Wanda suke kusa da tsohon ciyaman na PDP sun tabbatar da cewa Muazu yake da gida da EFCC suka gano miliyan $50

Kamfanin, a kan ‘website’ sun jera Mu'azu a matsayin maigidan. Amma a game da 9:00 na dare, lokaci na ‘Eastern’ a Amurka, wani Akin Oyegoke wanda ya kira kansa a matsayin mataimakin Muazu akan labarai ya kira dandalin Sahara Reporters daga Landan domin ƙaryatãwa game da cewa tsohon shugaban PDP ya mallaki ginin. "Mista Muazu bai mallaki wani gida a Ikoyi, fãce gidansa a titi na Walter Carrington, Victoria Island Legas," Oyegoke ya ce.

KU KARANTA: Hukumar EFCC na ci gaba da tozarta kotunan Najeriya

Kabad da wuta ba ya ci da aka boye kudin

Kabad da wuta ba ya ci da aka boye kudin

Ga tsabar kudi na kasar waje

Ga tsabar kudi na kasar waje

Ga maninki kudi na kasashen waje

Ga maninki kudi na kasashen waje

Ga yadda aka gyera kudaden

Ga yadda aka gyera kudaden

Ga jami'an da suka kirga kudin kan aiki

Ga jami'an da suka kirga kudin kan aiki

A halin yanzu, wanda suke kusa da tsohon shugaban PDP sun tabbatar da cewa shi ne mai dukiya.

Ku biyo mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da kuma twitter a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan NAIJ.com bidiyo na nuna wani yana cewa ya kamata a binne duk shugabanin Najeriya wuri guda

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel