Champions league: Real Madrid da Ronaldo sun kafa tarihi

Champions league: Real Madrid da Ronaldo sun kafa tarihi

– Real Madrid ta ba Bayern Munich kashi

– An tashi wasa da ci 1-2 a filin Arianz Arena

– Dan wasa Ronaldo ya zuba kwallaye 2 a raga

Champions league: Real Madrid tayi abin kwarai a Munich

Champions league: Ronaldo ya ramawa Real Madrid kwallo

NAIJ.com ke rahoto maku cewa Kungiyar Real Madrid ta doke Bayern Munich da ci 1-2 a gasar UEFA Champions league na zakarun Nahiyar Turai. Real Madrid dai ba ta saba samun galaba a kasar Jamus ba a gasar.

Dan wasa Cristiano Ronaldo ya jefa kwallaye 2 bayan Bayern Munich sun fara zurawa Real Madrid din kwallo guda. Ronaldo dai ya kafa tarihi inda ya zama duk Duniya babu mai yawan kwallayen sa a Gasar.

KU KARANTA: UCL: Juventus ta koyawa Barca darasi

Champions league: Real Madrid tayi abin kwarai a Munich

Koci Carlo Ancelotti da Zidane sun yi aiki tare a Real Madrid

Yanzu Ronaldo yana da kwallaye 100 a Gasar UEFA yayin da Real Madrid tayi wasanni 53 kullum sai ta jefa kwallo a ragar takwarorin ta. Yanzu dai Real Madrid za ta gamu da Bayern a gidan ta a wani makon.

Monaco ta ba Dortmund kashi yayin da ita ma Atletico Madrid ta doke Leicester City da ci guda mai ban haushi. Dama can kuna da labari Juventus ta ba Barcelona dan-karen kashi shekaran jiya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Efe yayi nasara a Gasar BBNaija

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel