Hukumar EFCC ta kuma babban kamu a jihar Lagas (HOTO)

Hukumar EFCC ta kuma babban kamu a jihar Lagas (HOTO)

- Hukumar EFCC tayi gagarumin aiki a wani gida dake Ikoyi

- An gano makudan kudi na kasashe daban daban

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta yi wani gagarumin aiki wanda ya kaisu ga samo wasu makudan kudi da aka boye a wani daki.

A cewar hukumar, an gudanar da aikin ne a ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu a wani daki a Ikoyi, jihar Lagas.

NAIJ.com ta rahoto cewa an gano makudan kudade a Naira, daloli da kuma fam (pounds) sannan kuma an debo ma’aikatan banki tare da injinan su don su taimaka gurin kirga kudaden.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nada daraktoci 5 a hukumar CBN

Masu leken asirin da hukumar EFCC ta kafa suna haifar da ‘ya’ya masu idanu a makonnin nan kamar yadda kwanan nan aka gudanar da aiki makamancin wannan a kasuwar Balogun wanda ya kai ga aka samo naira miliyan 250.

Hukumar EFCC ta kuma babban kamu a jihar Lagas (HOTUNA)

Hukumar EFCC ta kuma babban kamu a jihar Lagas

A cewar rahotanni, ba’a riga an chanja kudaden da aka samu a kasuwar Balogun zuwa kudaden kasar waje ba tukuna.

Hukumar tace a wani jawabi ta kakakin ta, Wilson Uwujaren, cewa kamun ya faru ne ta hannun wani da yayi tsegumi.

A cewar sanarwan, ba’a riga an chanja kudaden zuwa na waje ba a kasuwar Balogun dake jihar Lagas.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel