Gwamnatin tarayya ta tara N3.3 tiriliyan ta hanyar karbar haraji a 2016

Gwamnatin tarayya ta tara N3.3 tiriliyan ta hanyar karbar haraji a 2016

- Hukumar taara kuɗaɗen haraji ta tarayya FIRS ta tara naira tiriliyan 3.3 na kuɗaɗen haraji a shekarar 2016

- Shugaban hukumar Tunde fowler ya bayyana haka

Mista Fowler na nagana ne a wurin taron da aka shiryawa ƴan jaridu kan yadda zasu rika kawo rahoto akan harkar karɓar haraji.

Ya yaba da ƙoƙarin hukumar na tara waɗannan kuɗaɗe a lokacin da tattalin arzikin kasarnan yake cikin mawuyacin hali.

Ya yaba da ƙoƙarin hukumar na kaiwa wannan matsayi a lokacin da farashin gangar mai takai ƙasa da $50 cikin sama da watanni tara,a kuma lokacin da farashin hannayen jari yayi ƙasa a kasuwar hada-hadar hannun jari ta ƙasa.

Gwamnatin tarayya ta tara N3.3 tiriliyan ta hanyar karbar haraji a 2016

Gwamnatin tarayya ta tara N3.3 tiriliyan ta hanyar karbar haraji a 2016

NAIJ.com ta tsinkayi Fowler yana cewa sun faɗaɗa yin rijistar masu biyan haraji a faɗin ƙasa baki ɗaya na Sababbin masu biyan haraji,wanda hakan yakawo ƙarin mutane 814,000 masu biyan haraji, yayin da hukumomin haraji na jihohi sukayi rijistar mutane miliyan 3.

KU KARANTA: Ana neman a tsige Gwamnan Zamfara

Wasu dalilan da suka sa aka tara waɗannan makuɗan kuɗaɗe sun haɗa da haɗin kai tsakanin hukumar tara haraji ta bai ɗaya(JTB), da hukumomin tara haraji na jihohi ta bangaren rijistar masu biyan haraji,wayar da kan mutane kan biyan haraji,tattabatar da cewa anbiya haraji da kuma sauran dalilai.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma yan kasuwa ne ke bayyana yadda farashin kayayyaki suke shafar su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel