Matasa a shiyyar Kaduna ta Arewa sun fara shirin maido da Sanatan su

Matasa a shiyyar Kaduna ta Arewa sun fara shirin maido da Sanatan su

- Al'ummar Kaduna Ta Arewa Sun fara shirye-shiryen yiwa Senatan su kiranye

- Sun fara yin hakan ta hanyar da dokar kasa ta aminta dashi

Izuwa yanzu dai wadanda suka jefa wa Senata Suleiman Hunkuyi kuri'u a zaben da ta gabata sun fara janye kuri'ar su domin dawo dashi gida daga aiken da suka yimasa zuwa majalisa.

NAIJ.com ta samu labarin cewar kiranyen ya biyo bayan rashin iya wakilci da kuma kaucewa akan abunda suka wakilta shi yaje majalisar ya aiwatar.

In dai ba mu manta ba, kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bawa masu zabe damar janye kuri'ar su akan senata ko dan majalisar wakilai da suka tura majalisa muddin bukatar hakan ta taso.

Matasa a shiyyar Kaduna ta Arewa sun fara shirin maido da Sanatan su

Matasa a shiyyar Kaduna ta Arewa sun fara shirin maido da Sanatan su

A wani labarin kuma, Kungiyar kare hakkin bil'adama ta duniya, Amnesty International ta fitar da rahoton shekara ta 2016 kan zartar da hukuncin kisa a duniya

A cikin rahoton Amnesty ta ce an samu gagarumar raguwar mutanen da aka zartar wa hukuncin kisa a faɗin duniya.

KU KARANTA: Asirin Yakubu Dogara na daf da tonuwa

Sai dai Amnesty ta ce ko da yake an samu wannan sauyi, amma ba haka abin yake a China ba, wadda ƙungiyar ta zarga da zartar da gagarumin hukuncin kisa.

Ta ce mutanen da China ta zartar musu da hukuncin kisa a bara sun haura na sauran ƙasashen duniya idan aka haɗe su wajen guda.

NAIJ.com ta samu labarin cewa a karon farko cikin sama da shekara goma, Amurka ba ta cikin ƙasa biyar da suka fi amfani da hukuncin kisa a shekarar da ta gabata.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli yan Najeriya suna nuna fushin su ga gwamnati.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel