Ba kan ta: Wani Dan Majalisa na nema ya tonawa Dogara asiri

Ba kan ta: Wani Dan Majalisa na nema ya tonawa Dogara asiri

– Jiya ne Yakubu Dogara ya bayyana albashin da yake karba kowane wata

– Dama can Jama’a sun ce har yanzu Kakakin Majalisar bai bada gamsasshen bayani ba

– Wani Dan Majalisa dai yace da kyar idan takardun gaskiya Kakakin ya fitar

Ba kan ta: Wani Dan Majalisa na nema ya tonawa Dogara asiri

Hon. Jibrin na nema ya tonawa Dogara asiri

Honarabul Abdulmumin Jibrin wanda aka dakatar daga Majalisa tun bara yace akwai alamun tambaya a takardun da Yakubu Dogara ya fitar na albashin sa. Jibrin yayi wannan bayani ne a shafin sa na Twitter.

A jiya ne NAIJ.com ta kawo maku labari cewa ana ta sa-in-sa tsakanin Gwamna El-Rufa’i da Majalisa wanda har ta kai Gwamnan ya bayyana albashin sa kuma ya kalubalanci Majalisar tayi hakan.

KU KARANTA: Ana cigaba da hurowa Yakubu Dogara wuta

Ba kan ta: Wani Dan Majalisa na nema ya tonawa Dogara asiri

Takardun albashin shugaban Majalisa Dogara

Yakubu Dogara dai ya bayyana na sa albashin ko da yake Jama’a sun ce bai bada gamsashhen bayani game da alawsus din ‘Yan Majalisar ba. Sai ga shi ma dai Honarabul Jibrin yana cewa idan har takardun da Kakakin ya fitar ba na bogi bane, to albashin sa ya fi na shugaban Majalisar.

Jibrin yace yana nan zai fitar da takardun albashin sa kowa ya gani, ya kuma kara da cewa watakila ana tsula masa na sa albashin ne da kuskure don kuwa albashin sa ya fi na Dogara. Har yau dai Allah kadai ya san kasafin kudin Majalisun kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wai Majalisa na da wani amfani kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel