Rusau: “Saboda ni El-Rufai ya rusa ma inuwa Abdulkadir gida” – Shehu Sani

Rusau: “Saboda ni El-Rufai ya rusa ma inuwa Abdulkadir gida” – Shehu Sani

- Kwamared Shehu Sani ya jajanta ma Inuwa Abdulkadir sakamakon rusa masa gida da gwamnatin jihar Kaduna tayi

- Shehu Sani ya danganta rusa gidan da siyasa tsantsa ba wai doka ba

Sanata mai wakiltar al’ummar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani yace gwamnan jihar Kaduna ya rusa gidan mataimakin shugaban jam’iyyar APC ne saboda rikicinsa da gwamnan.

NAIJ.com ta ruwaito a satin data gabata ne hukumar kula da tsare tsaren gidaje na jihar Kaduna, KASUPDA tayi ciki da gidan mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen Arewa maso yamma Alhaji Inuwa Abdulkadir dake lamba 11 Yakubu Avenue cikin garin Kaduna.

KU KARANTA: ‘Mulkin El-Rufai daidai yake da tsarin APC’ – Inji shugaban APC Oyegun

Shehu Sani ya bayyana haka ne yayi wata ziyarar jaje daya kai ma Abdulkadir din a Abuja, inda yace: “A iya fahimta ta, abinda gwamnatin Kaduna tayi maka siyasa ce, kuma na tabbata an rusa maka gida ne saboda dagewar na ganin an tafiyar da jam’iyya akan turbar data dace, tare da ganin an tabbatar da gaskiya da bin doka a jam’iyya.

Rusau: “Saboda ni El-Rufai ya rusa ma inuwa Abdulkadir gida” – Shehu Sani

Inuwa Abdulkadir tare da Shehu Sani

“Sa’annan na san an rusa gidanka ne saboda ni, sakamakon kokarin daka yin a ganin an tabbatar da gaskiya a jam’iyyar APC musamman a jihar Kaduna, sai dai yayan jam’iyyar mu sun gamsu da kokarin naka. Na san da ace kayi abinda suke bukata daga gareka, ta hanyar zama dan koransu, toh da ba’a rusa maka gida ba.

Rusau: “Saboda ni El-Rufai ya rusa ma inuwa Abdulkadir gida” – Shehu Sani

Gidan Inuwa Abdulkadir

“Abin takaici ne ace wasu masu ikirarin su yan siyasa ne amma basa iya daukan suka, ya zama wajibi akan mu a matsayin mu na shuwagabanni da muka din karbar suka tare da jure masa.” Inji shi.''

Dayake mayar da jawabi, Inuwa Abdulkadir yace rusa masa ba zai hana shi gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba

“A yanzu haka maganan na kotu, don haka ba zan so in cika tsokaci akai ba, amma duk da haka ina so in tabbatar ma duk wani dan jam’iyyar APC cewa ba zan fasa duganar da ayyukan jam’iyya ba yadda na saba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Anyi bikin zuba hannun jari a Kaduna

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel