Akwai sauran rina a kaba: Yakubu Dogara ya bayyana albashin sa; sai dai…

Akwai sauran rina a kaba: Yakubu Dogara ya bayyana albashin sa; sai dai…

– Yakubu Dogara ya bayyana albashin sa amma fa har yanzu mutane sun ce akwai sauran aiki

– Jama’a su kace Kakakin Majalisar bai bada gamsasshen bayani ba

– Gwamna El-Rufai ne ya kalubalanci Majalisun kasar

Akwai sauran rina a kaba: Yakubu Dogara ya bayyana albashi; sai dai…

An fadawa Dogara cewa har yanzu bai yi komai ba

A jiya ne NAIJ.com ta kawo maku labari cewa Gwamna El-Rufa’i ya caccaki Majalisa wanda har kalaman na sa ba su yi mata dadi ba. Kakakin Majalisar ya maidawa Gwamnan martani nan take. Inda har ta kai Gwamnan ya bayyana albashin sa kuma ya nemi Majalisa tayi hakan.

Sai ga shi jiya Yakubu Dogara ya bayyana na sa albashin na kowane wata. Amma kuma Jama’a sun ce fa har yanzu ba ayi komai ba don kuwa an yi ba ayi bane a cewar su. Wasu dai sun ce abin da ake bukata shi ne Kakakin Majalisar ya bayyana kasafin su da alawas ba kurum albashin sa ba.

KU KARANTA: Idan na mutu a bizne ni da katin PDP-Inji Walid Jibrin

Akwai sauran rina a kaba: Yakubu Dogara ya bayyana albashi; sai dai…

Rt. Hon. Yakubu Dogara tare da shugaban kasa Buhari

Shi dai El-Rufai ya bayyana yadda ya kashe kudin harkar tsaro a Jihar sa. Rt. Hon. Yakubu Dogara ya soki Gwamnan Jihar Kaduna El-Rufai yace har yanzu shi ma bai bada cikakken bayanin da ake bukata ba.

Majalisa dai na karbar Naira Biliyan 115 a kowane shekara wanda har yau babu wanda ya san yadda ake yi da kudin. Gwamna El-Rufai yake cewa wannan kudi sun yi yawa don kuwa ba aikin da ‘Yan Majalisar ke yi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gwamnati na nema ta sa wani Bawan Allah ya fara sata

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel