Dogara ya bada bayanin albashinsa na watanni 6 daki daki

Dogara ya bada bayanin albashinsa na watanni 6 daki daki

- Kaakakin majalisa Yakubu Dogara ya bada bahasin albashinsa na watanni da dama

- Kaakakin majalisa na daukan albashin da bai gaza N206,577.87 a kowane wata ba

Dayake amsa kalubalen da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai yayi a gare shi, Kaakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya bayyana albashina daki daki tare da wasu bayanan kasafin kudin majalisar.

Kaakakin majalisar, Yakubu Dogara ya bayyana bayanan albashin ne a ranar Talata 11 ga watan Afrilu ta bakin mai magana da yawunsa, Turaki Hassan inda takardun suka nuna cewar ya amshi N346, 577.87 a matsayin albashin sa na watan Janairu.

KU KARANTA: An bayyana albashin gwamnan Jihar Kaduna

A watan Feburairu kuwa, Kaakakin majalisa Yakubu Dogara N206,577.87 ya samu, inda a watan Maris ya samu N276,577.87.

Dogara ya bada bayanin albashinsa na watanni 6 daki daki

Kaakakin Majalisa Yakubu Dogara

Dogara ya bada bayanin albashinsa na watanni 6 daki daki

Bayanin albashin Dogara

Idan dai ba’a manta, NAIJ.com ta kawo muku rahoton bayanan kasafin kudin kananan hukumomin jihar Kaduna da gwamna El-Rufai ya fitar, tare da bayani filla filla akan kudin tsaro da kuma albashinsa.

Dogara ya bada bayanin albashinsa na watanni 6 daki daki

Bayanin albashin Dogara

Da fari dai El-Rufai ne ya fara shawartar majalisar wakilai data fito fili ta bayyana ma yan Najeriya yawan kasafin kudinta, inda ya bukaci da su bayyana ma yan Najeriya cikakken bayani kan kasafin kudinsu na shekarar 2016 daya kai naira biliyan 115.

Dogara ya bada bayanin albashinsa na watanni 6 daki daki

Bayanin albashin Dogara

Sai dai a yayin wani taron manema labaru, mai magana da yawun majalisar ta wakilai Abdulrazak Namdas yace gwamna El-Rufai ya bada bayanin kasafin kudin tsaron jihar Kaduna ne ba wai kudaden da aka ware na tsaron gwamna ba, kamar yadda Dogara ya bukata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda Sarkin Kano ya ja hankulan shuwagabannin Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel