Matar data haifi yan 4 ta samu tallafi daga matar gwamna

Matar data haifi yan 4 ta samu tallafi daga matar gwamna

- Uwargidar gwamnan jihar Bauchi Hadiza Mohammed Abubakar ta kai agaji ga matar data haifi yan 4

- Uku cikin jariran da malama Huzaifatu ta haifa sun rigamu gidan gaskiya

Sakamakon neman taimako da aka yi ma matar nan data haifi yan 4 a garin Katagum na jihar Bauchi, mai suna Huzaifatu, Uwargidar gwamnan jihar ta dauki nauyin kulawa da ita.

A ranar Litinin 10 ga watan Afrilu ne uwargidar gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar ta aika da tawagar wakilanta karkashin jagorancin matar shugaban hukumar Katagum don su duba halin da mai jegon take ciki.

KU KARANTA: Ganduje ya taimaka ma Sojoji da sabbin motoci 16 (Hotuna)

Sai dai uku daga cikin jariran sun rigamu gidan gaskiya, kamar yadda NAIJ.com ta samu rahoto daga asibitin gwamnatin tarayya dake garin Azare.

Matar data haifi yan 4 ta samu tallafi daga matar gwamna

Malama Huzaifatu, uwar yan 4

Uwargidar gwamnan zata kai ziyarar ta’aziya ga matar sa’annan ta umarci hukumar babban asibitin dake garin Azare dasu baiwa matar dukkanin kulawar data dace don ganin sun ceci rayuwar jaririya daya data rage daga cikin yan hudun, kuma ta dauki nauyin dukkanin dawainiyar ta.

Ga hotunan wasu cikin jariran:

Matar data haifi yan 4 ta samu tallafi daga matar gwamna

Jaririya

Matar data haifi yan 4 ta samu tallafi daga matar gwamna

Jaririya

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda wata mata ke kuka bayan an sace kwashe mata yaranta

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel