Majalisa ta maka ma ministan Buhari taran naira miliyan 1

Majalisa ta maka ma ministan Buhari taran naira miliyan 1

- Majalisar dokokin jihar Ekiti ta ci minista Kayode Fayemi taran N1m

- Fayemi ya ce ba zai gurfana gabanta ba, kuma ba zai tanka gwamna Fayose ba

A ranar Talata 11 ga watan Afrilu ne majalisar dokokin jihar Ekiti ta ci tsohon gwamnan jihar, kuma ministan tama da karafa a yanzu Mista Kayode Fayemi taran naira miliyan guda.

Majalisar tace ya zama wajibi taci Fayemi tarar sakamakon rashin amsa sammacin da suka aika masa naya gurfana gabanta har sau uku.

KU KARANTA: “Ina so a binne ni tare da katin PDP kabarin PDP” – Sanata Walid Jibrin

Jaridar Punch ta ruwaito cewar majalisar ta yanke shawarar cin sa tarar ne a zaman data yi a ranar Talata 11 ga watan Afrilu.

Majalisa ta maka ma ministan Buhari taran naira miliyan 1

Minista Kayode Fayemi

NAIJ.com ta ruwaito Fayemi ya dade yana artabu da gwamnatin jihar Ekiti karkashin gwamna Fayose tare da majalisar jihar. Sai dai mataimakin ministan ta fannin watsa labaru Yinka Oyebode yaki amsa kirar da NAIJ.com tayi masa ta wayar tarho don jin ta bakinsa.

Amma ko a baya ma can, Minista Fayemi yayi alkawarin ba zai tanka duk wani hargowar da majalisar jihar Ekiti keyi ba ko ma na gwamnatin jihar.

Majalisa ta maka ma ministan Buhari taran naira miliyan 1

Fayemi da Fayose

Fayemi ya bayyana ma yan jaridu cewa: “Kun san ba zan taba tanka gwamna Fayose ba, yana da ikon fadin ra’ayinsa, don haka ya cigaba da jin dadin rahar da yake yi. Amma idan lokaci yayi, zai ga sakamakon hakan.”

Fayemi yacigaba da fadin: “Kun san ni ba dan tasha bane, don haka ba zan bari ya jani cikin tabo ba. Gaskiya day ace, kuma ai rana bata karya.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana gwarama a kudancin Najeriya, kalli wani mutum da yayi ikirarin allanta

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel