Shugaban FRSC yayi ma jami’an hukumar mata aski (Hotuna)

Shugaban FRSC yayi ma jami’an hukumar mata aski (Hotuna)

- Kwamandan hukumar kare haddura ya aske ma jami'an hukumar mata gashin kai

- Kwamandan yace yayi haka ne don hukunta masu yin duk shiga da suka ga dama

Kwamandan hukumar kare haddura ta kasa, FRSC reshen jihar Ribas, Andrew Kumapayi ya kaddamar da wani aiki na musamman akan jami’an hukumar yan mata.

Kwamandan ya kaddamar da aikin hukunta duk jami’in daya kama basa sanye da cikakken kayan aikin hukumar ba.

KU KARANTA: An dakatar da shugaban FRSC kan yi wa mata askin dole

Inda a ranar Litinin 10 ga watan Afrilu ya binciki wasu jami’an hukumar musamman ya duba kumbunansu, tare da kayan sarki.

Shugaban FRSC yayi ma jami’an hukumar mata aski (Hotuna)

Yayin da ake yi ma jami'an aski

Daga nan ne ya bukaci a bashi almakashi, inda ya fara yanke gashin wasu jami’an hukumar mata, wadanda yace kwalliya jami’an suke yi da su.

Shugaban FRSC yayi ma jami’an hukumar mata aski (Hotuna)

Aski ba kama hannun yaro

Sai dai tuni Shugaban hukumar Boboye Oyeyemi ya bayar da izinin dakatar da Mista Andrew A. Kumapayi tare da matan da ya yankewa gashin nasu, don a gudanar da bincike kan lamarin.

bugu da kari NAIJ.com ta jiyo ra'ayoyin jama'a da dama da suka dinga sukar wannan, kwamanda tare da yin Allah wadai da abinda ya aikata.

Ga sauran hotunan nan:

Shugaban FRSC yayi ma jami’an hukumar mata aski (Hotuna)

Askii

Shugaban FRSC yayi ma jami’an hukumar mata aski (Hotuna)

Wadanda aka yi ma aski

Shugaban FRSC yayi ma jami’an hukumar mata aski (Hotuna)

Gashin da aka aske

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kunga wani dan Biafra da yayi ikirarin allantaka? kalla a nan:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel