Shari’a da talauci: An maidawa Sarkin Kano Sansusi II martani

Shari’a da talauci: An maidawa Sarkin Kano Sansusi II martani

– An maidawa Sarkin Kano Sanusi II martani game da kalaman sa

– Sarki Muhammadu Sanusi II yace Jihar Zamfara na fama da talauci a dalilin dabbaga shari’a

– Wani mai nazari yace akwai sake a maganar Sarkin

Shari’a da talauci: An maidawa Sarkin Kano Sansusi II martani

Sarkin Kano Muhammadu Sansusi II

Idan ba ku manta ba kwanaki NAIJ.com ta kawo maku labari wasu Jama’a dai sun fara ganin cewa kalaman Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na nema ya wuce gona da iri. Mai girma Sarki Sanusii II ya bayyana cewa Arewacin Najeriya sun fi ko ina talauci a kasar.

Wani mai nazari Dr. P. Brima yayi raddi ga kalaman Sarki inda yace Jihar Zamfara ta fi kowace Jiha talauci a Najeriya a dalilin dabbaga shirin shari’ar musulunci. Wannan mutumi yake cewa bai dace irin Sarki ya furta wannan kalamai da za su ayi masa mummunar fassara ba.

KU KARANTA: Ana sukar kalaman Sarkin Kano Sanusi II

Shari’a da talauci: An maidawa Sarkin Kano Sansusi II martani

An yi wa Sarkin Kano Sansusi II raddi

Dr. Brimah yake cewa babu watta hujja da za ta gaskata kalaman Sarkin yake cewa babu tabbacin cewa ma Jihar Zamfara ce ta fi ko ina talauci a Najeriya don wasu alkaluman dabam suna nuna cewa Jihohin Yobe da Sokoto ko Kebbi da Bauchi ne kan gaba.

Tun dai a lokacin da Sarkin yayi magana Farfesa Ango Abdullahi ya maida masa martani inda yace masa shi yaro ne wanda yake bukatar ya koma ya karanta tarihin Arewa. Wasu dai suna ganin Sarkin a matsayin mai fadin gaskiya komai dacin ta inda wasu ke ganin azarbabi gaare sa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya caccaki shugabanni

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel