Gobara ta ci hedikwatar hukumar kula da sifirin jiragen sama na Najeriya

Gobara ta ci hedikwatar hukumar kula da sifirin jiragen sama na Najeriya

- Hedikwatar hukumar da ke kula da sifirin jiragen sama a Najeriya (FAAN) dake jihar Lagas ya kama gobara a ranar Talata, 11 ga watan Afrilu

- Kwamishinan yan sandan jihar Lagas, Fatai Owoseni, ya jagoranci sauran jami’ai zuwa gurin da abun ya faru sannan kuma ya shiga daga cikin masu kokarin taimako

Ginin hukumar da ke kula da sifirin jiragen sama a Najeriya (FAAN) dake jihar Lagas ya kama gobara, wani rahoto daga The Sun.

NAIJ.com ta samu labarin cewa gobarar ya fara ne da safiyar ranar Talata, 11 ga watan Afrilu, 2017 wanda ya jawo asarar kayayyakin miliyoyin naira.

Tuni dai sashen kashe gobara na hukumar tare da hadin gwiwar hukumar kashe gobara na jahar Lagos suka shawo kan al’amarin.

Gobara ta ci hedikwatar hukumar kula da sifirin jiragen sama na Najeriya

Gobara ta ci hedikwatar hukumar kula da sifirin jiragen sama na Najeriya

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa bayanai sun bayyana cewa wutar wanda ya fara ci da karfe 8:30 na safe ya sanya ma’aikata da dama cin na kare daga ofishin su don tsira.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da shugaban FRSC kan yi wa mata askin dole

Har yanzu ma’aikatan FAAN basu bayar da jawabi ba a lokacin da ake kawo wannan rahoton.

Kwamishinan yan sandan jihar Lagas, Fatai Owoseni, ya jagoranci sauran jami’ai zuwa gurin da abun ya faru sannan kuma ya shiga daga cikin masu kokarin taimako.

A halin yanzu, kalli bidiyon NAIJ.com na yadda aka rufe filin jirgin sama na Abuja yayinda gwamnatin tarayya ta fara aikin gyare-gyare:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel