Kotu ta aika da makafi 2 yan luwadi gidan kaso a garin Minna

Kotu ta aika da makafi 2 yan luwadi gidan kaso a garin Minna

-Kotu ta yanke ma wasu makafi yan luwadi zaman gidan yari shekaru uku uku

-Makafin yan luwadin suna yaudarar kananan yara da kudi don aikata ashsha dasu

Wata kotun majistiri dake zaune a garin Minna babban birnin jihar Neja, ta yanke ma wasu makafi su biyu hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bayan ta kama su da laifin aikata luwadi da wasu kananan yara biyu masu shekaru 10 da 12.

Kotun ta yanke ma makafin biyu 'yan luwadi wannan hukuncin ne a ranar Alhamis 6 ga watan Afrilun 2017 sakamakon samunsu da laifin cin zarafin kananan yara ta hanyar Luwadi, sa’annan kotun bata basu zabin biyan tara ba.

KU KARANTA: Farfesa Ango Abdullahi ya mayar da martani ga Sarkin Kano

Kamfanin dillancin labaru ta Najeriya, NAN ta ruwaito cewar Alkaliya mai shari'a Hajiya Hauwa ta yanke masu wannan hukuncin ne bayan wadanda ake zargi makaho Idris Usman da makaho Abubakar Saddik sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa bisa radin kansu, daga nan ne Alkaliya ta yanke ma kowanin su hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Kotu ta aika da makafi 2 yan luwadi gidan kaso a garin Minna
Barista Maryam Haruna Kolo

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewar jami'in dansanda mai gabatar da kara, Abdullahi Mayaki ya shaida ma kotun cewar wadanda ake zargin sun aikata laifin ne tun a watan disambar 2016, sun kuma rudi yaran ne da kudi naira 50 da naira 100 ne sannan suka aikata luwadin da su, inji shi.

Dansanda mai kara, Abdullahi Mayaki ya cigaba da cewa laifin da suka aikata ya sabawa sashi na 19 na kundin dokokin kare hakkin yara na Jihar Neja, bisa ga doka wadanda ake zargin za'a yanke masu hukuncin daurin shekaru 14 ne, amma anyi masu sassaucin hukuncin ne saboda sun amsa laifin su sannan sun nemi sassauci daga kotu-cewar Mayaki.

Daraktar hukumar kare hakkin yara na Jihar Neja Barista Maryam Haruna Kolo wacce take a kotun yayin da ake sauraron karar ta yaba da wannan hukunci, ta kuma jinjinawa kotun akan tabbatar da gaskiya dan gane da wannan shari'a.

“Ina fata wannan hukuncin zai zama darasi ga masu kokarin aikata haka anan gaba.” inji ta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda wani mutum ya kwashe ma wata mata gaba daya yaranta

Asali: Legit.ng

Online view pixel