Ganduje ya taimaka ma Sojoji da sabbin motoci 16 (Hotuna)

Ganduje ya taimaka ma Sojoji da sabbin motoci 16 (Hotuna)

- Gwamnatin jihar Kano ta taimaka ma rundunar sojoji da kayayyakin aiki

- Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya jagoranci bikin bayar da motocin aikin ga sojoji

Gwamna jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa rundunar Sojojin Najeriya reshen jihar Kano sababbin motoci guda 16 tare da gyara musu tsofaffin da suka lalace.

Gwamna Ganduje da kansa ya jagoranci bikin bada motocin har guda 16 kirar toyota Hilux, yayinda kwamandan rundunar sojoji reshen jihar Kano ya amsa makullan motocin a madadin hukumar soji.

KU KARANTA: Rundunar soji ta hallaka yan Boko Haram 57

NAIJ.com ta ruwaito bikin raba motocin dai ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin 10 ga watan Afrilu.

Ganduje ya taimaka ma Sojoji da sabbin motoci 16 (Hotuna)

Ganduje yayin dayake mika makullan motocin ga kwamandan soji

A jawabin gwamnan, yace gwamnatin jihar Kano ta baiwa sojojin motocin ne don saukaka musu aikace aikacen sun a tsaron lafiya da dukiyoyin al’ummar jihar.

Ganduje ya taimaka ma Sojoji da sabbin motoci 16 (Hotuna)

Sabbin motoci 16

Sa’annan ya bukace su dasu zage damtse wajen tabbatar da ganin sun gudanar da aikinsu yadda ya kamata ba tare da cin zarafin jama’a ba.

Ganduje ya taimaka ma Sojoji da sabbin motoci 16 (Hotuna)

Ganduje yayin dayake jawabi

Dayake nasa jawabin, Kwamandan soji ya gode ma gwamnatin jihar Kano, sa'annan yayi alkawarin sojoji zasu cigaba da kyautata tsaro a duk fadin jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon yadda wani jami'in tsaro ya harbe wata mata a bisa kuskure

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel