An kama masu bara da dama a Jihar Kano

An kama masu bara da dama a Jihar Kano

– Gwamnatin Jihar Kano ta kama masu bara fiye da 400 a cikin Garin

– Hukumar Hisbah ce dai tayi wannan aiki a fadin Jihar

– Dama Sarki Muhammadu Sanusi II yace Arewacin Najeriya sun fi ko ina talauci

An kama masu bara da dama a Jihar Kano

Akwai Almajirai miliyan 3 a Jihar Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama masu bara da roko a Jihar Kano da dama cikin watan jiya da shekaran jiya kamar yadda NAIJ.com ke samun labari yanzu haka. An dai kafa dokar da ta haramta bara a cikin Garin Kano.

Shugaban Hukumar Hisbah Malam Musa Tsangaya ya bayyanawa manema labarai wannan. Tsangaya yace an kama masu bara ne a cikin Garin wanda ya saba doka. Cikin dai wanda aka kama akwai manyan mutane kusan 200 yayin da sauran kuma kananan yara ne.

KU KARANTA: Yar shekara 4 ta haihu a Jihar Bauchi

An kama masu bara da dama a Jihar Kano

Arewacin Najeriya sun fi ko ina talauci-Sarki Muhammadu Sanusi II

Mafi yawan wadanda aka kama dai ‘Yan asalin Jihar Kano ne yayin da sauran kuma su ka fito daga Jihohin Kaduna da Jigawa masu makwabtaka da Kano. Cikin wadanda aka kama dai har da maras hankali.

Kwanan nan Sarkin Kano ya bayyana cewa Arewacin Najeriya sun fi ko ina talauci a wani taro da aka yi a Kaduna. Wasu dai sun fara ganin cewa kalaman Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na nema su wuce gona da iri.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda farashin kaya su ka tashi a kasuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel