Gwamnatin Buhari za ta kammala titin jirgin kasan Abuja a cikin watan Oktoban 2017

Gwamnatin Buhari za ta kammala titin jirgin kasan Abuja a cikin watan Oktoban 2017

- Babban dan kwangilar da ke aikin titin jirgin kasa na kai-da-kawo da zirga-zirgar jirgin a Abuja

- Ya bayyana wa Ministan Abuja, Muhammad Bello cewa za a kammala aikin titin jirgin kasan nan da watan Oktoba mai zuwa

- Yayin da za a fara gwada hawan titin a cikin watan Nuwamba

Ministan ya bayyana wa wata tawagar kungiyar masu kula da harkokin yawon bude ido ta kasa wannan bayani ne yayin wata ziyara da suka kai masa.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Kungiyar a karkashin jagorancin shugaban ta Tomilola Akingbogun ne suka kai wa ministan ziyara a ofishin sa da ke shiyyar Garki 1, Abuja.

Ministan ya ce kamar yadda ya samu tabbaci daga dan kwangilar da ke aikin, za a fara zirga-zirga ka’in da na’in a cikin watanni uku na farkon shekara ta 2018.

Titin jirgin kasan Abuja

Titin jirgin kasan Abuja

Ya kuma ce an kafa kwamiti domin ya duba matsalar karbar haraji a Abuja sannan yayi kira da a yawaita gina kananan dakunan baki masu arha saboda yawan baki da suke shigowa garin Abuja.

KU KARANTA: Wani dan Katsina mai zana kayatattun motoci (Hotuna)

Ya ce samun gudanar da ayyukan masu masana’antun kansu da sauran nau’o’in hada-hadar kasuwanci a Abuja, abu ne mai muhimmanci, don haka za su gaggauta duba matsalar yawan tsawwala haraji a cikin babban birnin tarayya.

A karshe ya ce tilas a ba harkokin yawon bude ido muhimmanci a Abuja domin a samu walwala da sukunin tafiyar da su.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli yadda ake tafiya a jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel