Abubuwa 6 game da Dangote yayin murnar cika shekaru 60 da haihuwa

Abubuwa 6 game da Dangote yayin murnar cika shekaru 60 da haihuwa

- Shahararren dan kasuwar nan Alhaji Aliko Dangote ya yi bikin cika shekaru 60 da haihuwa

- Dangote ya kasance wanda ya fi kowa arziki a kasar Afirka kuma 67 a duniya

Shahararren dan kasuwar nan Alhaji Aliko Dangote (GCON), an haife shi ne 10 ga watan Afrilu 1957 a garin Kano, kuma shine wanda ya mallaki Dangote Group.

Ya kuma mallaki kamfanoni aiki da dama a Najeriya da sauran kasashen Afirka, ciki har da Benin, da Habasha, Senegal, Kamaru, Ghana, Afrika ta kudu, Togo, Tanzania, da kuma Zambia.

Aliko Dangote ya yi bikin murnar zagayowar haihuwarsa a ranar Litini, 10 ga watan Afrilu yayin da ya cika shekaru 60 da haihuwa.

Abubuwa 6 game da Dangote yayin murnar cika shekaru 60 da haihuwa

Shahararren dan kasuwar nan Alhaji Aliko Dangote

Saboda haka NAIJ.COM ta yanke shawarar kawo wasu abubuwa 6 musamman game da Alhaji Aliko Dangote:

1. Aliko Dangote ne ya fi arziki a kasar Afirka tare da daraja kusan dala Amurka biliyan 21

Alhaji Aliko Dangote yana a matsayin 67 a cikin mutanen da suka fi kowa arziki a duniya kuma ya kasance wanda ya fi kowa arziki a kasar Afirka, kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa.

2. Aliko Dangote ya taba yin bauta a karkashin kawunsa

Dangote ya yi aiki a karkashin wani dan uwarsa, Sani Dangote. Ya yi aiki da kyakyawar aniya inda ya koya kwarewa, basira da kuma amincewa.

3. Dangote ya karbi aron kudi daga kawunsa domin ya fara kasuwanci

Aliko Dangote ya fara kasuwanci da kudin aro 500,000 wanda ya karba daga kawunsa. Ya gana da kawunsa a shekara 1977, kuma ya gaya masa game da shirinsa na yi kasuwanci sayar da kayayyaki kuma kawunsa ya ba shi rance da ya fara kasuwancin. Duk da haka, kawun ya bashi wa'adin wata uku da ya mayar da rance, kuma Dangote ya cika alkawarin.

4. Dangote ya fara kasuwancisa da shigowa da kayayyaki daga kasar waje

Ya fara kasuwancisa da kayayyaki kamar sugar, da shinkafa, da taliya, gishiri, auduga, da gero, koko, yadi da kuma kayan lambu. Yana shigo da wadannan kayayyaki ne daga kasasshen waje.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 5 da ya kamata matasan Najeriya su koya daga rayuwar Dangote

5. Dangote ya motsa daga shigowa da kayayyaki zuwa masana'antu bayan wasu shekaru kagan

Aliko Dangote ya fara sarrafa wasu daga cikin kayayyakin da ya ke shigowa da su a nan kasar.

6. Dangote ya kasanace kuma a harkar siyasa

Aliko Dangote ya shiga harkar siyasa inda ya bayar da dalla miliyan 2 ga tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ta yakin neman zabe a karo na biyu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon farashin kayayyaki a kasuwanni

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel