Kuskure! Gwamnatin ya ki biya biliyan N5 diyya ga iyalan 50 da harin bam na soji ya shafa

Kuskure! Gwamnatin ya ki biya biliyan N5 diyya ga iyalan 50 da harin bam na soji ya shafa

- Malami, SAN zai kalubalanci wani hukunci dake neman diyya

- Harin bom da sojin sama suka aikata a sansanin Rann a ranar 17 ga watan Janairu

- Zai kalubalantar kotu da cewa ba su da iko na jin maganan

- Ya ce basu amsa da wuri domin ofishin basu san al'amarin na kotu

Babban mai shari'a na tarayya (AGF) da kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, SAN

Babban mai shari'a na tarayya (AGF) da kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, SAN

Babban Mai Shari'a na Tarayya (AGF) da kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN zai kalubalanci wani hukunci dake neman diyya ga wadanda ke fama da harin bom da sojin sama suka aikata a sansanin Rann a ranar 17 ga watan Janairu.

KU KARANTA: Ko ka san nawa ne albashin Gwamna El-Rufa’i a duk wata?

Tijani Gazalli, wani babban lauya na gwamnati, jiya ya tambayi wani babbar kotun tarayya da ke Abuja ya kara masa lokaci domin ya zo da 'ƙin yarda' na farko da zai kalubalantar kotu da cewa ba su da iko na jin maganan hakkokin dake gaban su.

Gazalli yace ya kamata a ji maganan a jihar Borno, inda lamarin ya faru, ya kara da cewa mai nema ya rasa wuri tsaye na kawo maganan, tun kuma bai san wadanda ke fama da harin bom.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: EFCC ta bankado wata sabuwar N250 million jibge a cikin kasuwan Balogun

Ya ce basu amsa da wuri domin ofishin basu san al'amarin na kotu, ya kuma roki kotu kar su azabta jinkirta da sun yi na bata lokaci ba.

NAIJ.com ya ruwaito cewa, Hameed Ajibola Jimoh, ya ja gwamnatin tarraya kotu a watan Fabwairu da dalili cewa ya kamata gwamnati ya biya miliyan N100 ga iyalan kowane daga cikin sama da 50 wadanda suka rasu da kuma miliyan N50 ga wadanda suka ji rauni a harin bam din, wanda ya faru a Rann, na Jihar Borno.

A halin yanzu, alƙali John Tsoho ya umarci ofishin AGF su biya kudin ƙin cika alƙawari ga kotu ya kuma tura jin magana zuwa 28 ga watan Afrilu.

Ku biyo mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da kuma twitter a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan bidiyo na NAIJ.com na tambaya ya zai kasance idan Donald Trump ya kai hari ga 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel