Abin da ya dace da ni shine shugaban kasa, ba gwamna ba, inji Okorocha

Abin da ya dace da ni shine shugaban kasa, ba gwamna ba, inji Okorocha

- Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yace kujerar shugaban kasar tarayyan Najeriya ta fi dacewa da shi

- Yace ba zai yi takara da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba a 2019

- Rochas ya sha alwashin tsayawa takara bayan Buhari ya kammala wa'adin mulkin sa

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yace yana ganin kujerar shugaban kasar tarayyan Najeriya yafi dacewa da shi fiye da zama gwamna.

Abin da ya dace da ni shine shugaban kasa, ba gwamna ba, inji Okorocha

Rochas Okorocha yace shugabancin tarayyan Najeriya yafi dacewa da shi fiye da gwamna

A jiya Litinin, 10 ga watan Afrilu, Okorocha ya fada wa manema labarai a Owerri cewa ya rigada ya yanke shawarar cewa ba zai yi takara da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugabancin kasa na 2019 ba, amma zai gabatar da kansa don matsayin bayan karshen wa’adin mulkin Buhari.

KU KARANTA KUMA: Gwamna El-Rufa’i ya jikawa Kakakin Majalisa aiki

Yace: “Kujerar gwamna bai dace da ni ba. abunda ya dace dani shine shugaban kasar tarayyar Najeriya. Bazan yi takara da Buhari ba"

A halin da ake ciki gwamnatin jihar ta kaddamar da ranar 6 ga watan Mayu a matsayin ranar yancin kai.

Okorocha ya bukaci mutanen Imo da su halarci gurare da musamman inda zasu samu damar bayyana ra’ayoyinsu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wani mutumi da yayi barazanar yin sata idan abubuwa basu yi daidai ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel