Zamu cigaba da hana shigowa da shinkafa a Najeriya - Inji Kanal Hamid Ali

Zamu cigaba da hana shigowa da shinkafa a Najeriya - Inji Kanal Hamid Ali

- Shugaban hukumar kwastam ta kasa watau Comptroller General of Customs (CGC) Kanal Hameed Ali mai ritaya yayi magana

- Shugaban ya bayar da umurnin kara tsaurara matakai don ganin an hana shigowa da shinkafa ta kan iyakokin kasar nan.

Kanal Hamid Ali

Kanal Hamid Ali

NAIJ.com ta tsinkayi Mai magana da yawun hukumar ta Kwastam Mr Joseph Attah yana bayyana hakan a wata fira da yayi da majiyar mu inda yace kawo yanzu hukumar ta kwace buhunna shinkafa da suka kai yawan 250,825 da aka shigo da su ta barauniyar hanya a cikin shekarar da ta gabata.

Mai magana da yawon hukumar huma yace a cikin wata 3 kuma da suka wuce na wannan shekarar yanzu haka an kwace buhunna 921.

KU KARANTA: Ana fargabar bullar cutar zazzabin Lassa

A wani labarin kuma, Gwamnatin jahar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ta ce ta shirya don ta kwaso ‘yan gudun hijrar kasar kimanin dubu saba’in da takwas gida daga kasar Kamaru.

Dubban ‘yan gudun hijrar na daga cikin wadanda tsananin rikicin Boko Haram ya tilastawa tserewa gidajensu inda suka nemi mafaka a makwabciyar kasar.

A makon da ya gabata ma dai ‘yan gudun hijrar sun yi barazana takawa da kafarsu daga Kamaru zuwa Najeriya muddun gwamnati ta ki mutunta bukatarsu ta mayar dasu garuruwansu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma ana jin ra'ayoyin yan kasuwa ne game da farashin kayayyaki ciki hadda Shinkafa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel