Sanata Shehu Sani ya kalubalanci Sarkin Kano Muhammadu Sanusi

Sanata Shehu Sani ya kalubalanci Sarkin Kano Muhammadu Sanusi

- Shehu Sani ya bukaci Sarkin Kano daya bayyana sunayen mutanen da suka lahanta Arewa – Sarkin Kano yayi gargadin idan Arewa ta cigaba a haka, zata zama matalauciyar yanki

- Sanata dake wakiltar al’ummar Kaduna ta tsakiya kwamared Shehu Sani ya bayyana cewar mutanen Arewa sun gaji da yadda ake basu labarin talaucin su, kamata yayi a sama musu da mafita

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi

Rashin cigaba a Arewa: ‘Mun gaji da surutu, mafita muke nema’ – Shehu Sani, yayi wannan magana ne biyo bayan batun da ake danganta shi da Sarki Sanusi din.

NAIJ.com ta tsinkayi Sarkin Kano Muhammadu Sunusi inda yake cewa: “Idan da za’a raba Najeriya, da lallai yankin Arewa ne zasu fi kowa talauci. ”Sa’annan Sarkin ya kara da cewa Gwamnonin ba su da aikin yi sai zuwa Kasar China domin su karbo bashi.

KU KARANTA: Ku kalli hotunan wani dan Arewa nan da ya kware wajen zanen motoci

Mai martaban yace akwai gyara a lamarin kasar.

Mai martaba Sai dai wadannan kalamai basu yi ma Shehu Sani dadi ba, inda ya bayyana a shafin sa na Twitter yana fadin: “Yawan fadan yadda Arewa taci baya, wannan duk labara ne, amma ka fada mana su waye suka mayar da Arewa baya, shine ka cika gwani.''

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli yadda Sarki Sanusi yayi raga-raga da yan siyasar Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel