Fani Kayode ya soki Sheikh Gumi kan cewa da yayi Kiristoci ne suka bari ta’addanci ya bunkasa a Najeriya

Fani Kayode ya soki Sheikh Gumi kan cewa da yayi Kiristoci ne suka bari ta’addanci ya bunkasa a Najeriya

- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Fani Kayode ya kai hari Sheik Gumi kan sharhi da yayi a kan ta'addanci

- Babban malamin musulunci dake zaune a Kaduna Ahmed Gumi ya bayyana cewa musulmai ne kawai zasu iya yakar yan ta’addan Boko Haram dake ta’addanci a yankin Arewa maso gabashin Najeriya da ma duniya baki daya

- Amma Fani Kayode ya dage cewa Kiristoci sun sha wahala da kisan kare dangi a arewa tun 1966

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na kasar, Femi Fani Kayode ya yi Allah wadai da Sheikh Ahmad Gumi kan cewa da yayi Musulmai ne kawai zasu iya kawo karshen ta'addanci a Najeriya.

Fani Kayode ya soki Sheikh Gumi kan cewa da yayi Kiristoci ne suka bari ta’addanci ya bunkasa a Najeriya

Fani Kayode ya soki Sheikh Gumi kan cewa da yayi Kiristoci ne suka bari ta’addanci ya bunkasa a Najeriya

NAIJ.com ta tattaro cewa Malamin ya ce musulmai ne kawai zasu iya yakar yan ta’addan Boko Haram dake ta’addanci a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Duk dan majalisar da ya yi yunkurin tsige Buhari a bakacin kujerarsa - Inji Kwankwaso

Babban malamin musulunci dake zaune a Kaduna Ahmed Gumi ya bayyana cewa musulmai ne kawai zasu iya yakar yan ta’addan Boko Haram dake ta’addanci a yankin Arewa maso gabashin Najeriya da ma duniya baki daya.

Ya ce abun bakin ciki ne cewan mutane da dama basu san gaskiyar addinin Islama ba, sannan kuma wadannan mutanen sun bari jahilcin su ya jagorance su ta hukuncin su da sharhin su kan al’amuran da ya shafi addinin.

Da yake magana a gurin bikin yaye dalibai a makarantar koyan alakar musulmai da Kirista (Kaduna Centre for Study of Christian-Muslim Relations), Gumi, babban shehi yace akwai bukatar hadin kai tsakanin sauran addinai da Musulmai domin kawo karshen ta’addanci.

Cikin sharhi kan maganar Gumi da yayi a shafin Twitter, Fani Kayode yace: “Kiristoci sun sha wahala da kisan kare dangi a arewa tun 1966. Sheikh Gumi ya rufe bakin sa ya kuma sauke kansa cikin jin kunya sannan kuma ya daina kai hari ga Kiristoci.”

“An kashe Kiristoci da dama a arewacin Najeriya fiye da ko ina a duniya cikin shekaru 67 da suka shige. Baza’a yarda da wannan ba."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyon na NAIJ.com wanda wani dan Najeriya ke korafi game da halin da kasar ke ciki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel