Siyasar Kano: Anyi bikin kona Jar hular Kwankwasiyya a Kano (Hotuna)

Siyasar Kano: Anyi bikin kona Jar hular Kwankwasiyya a Kano (Hotuna)

- Gungun matasa sun sauya akidar siyasa daga Kwankwasiyya zuwa Gandujiyya

- An yi gangamin kona jar hula a jihar Kano

Wasu gungun matasa a jihar Kano sun ce sun yar da kwallon mangwaro don su huta da kuda, inda suka sauya akidar siyasa daga Kwankwasiyya zuwa Gandujiyya.

Siyasar Kano: Anyi bikin kona Jar hular Kwankwasiyya a Kano (Hotuna)

Siyasar Kano: Ganduje da Kwankwaso

Kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito, matasan da suka fito daga karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano sun yi wannan wankan tsarki ne a ranar Lahadi 9 ga watan Afrilun shekarar 2017, inda suka ce basu da wani dalilin cigaba da kasancewa a tsarin Kwankwasiyya.

KU KARANTA: Sojoji sun gina ma fararen hula Asibiti da famfon ruwa

Siyasar Kano: Anyi bikin kona Jar hular Kwankwasiyya a Kano (Hotuna)

Anyi bikin kona Jar hular Kwankwasiyya a Kano

Matasan sun bayyana ra’ayinsu na tarewa a inuwar Gandujiyya sakamakon sharbar romon dimukradiyya da suka ce sun yi a karkashin mulkin mai girma gwamna Abdullahi Ganduje, shugaban tsagin Gandujiyya.

Siyasar Kano: Anyi bikin kona Jar hular Kwankwasiyya a Kano (Hotuna)

Matasa da jar hula

Majiyar NAIJ.com ta dauko muku hotunan gungun matasan a lokacin da suke gudanar da bikin kona jajayen hulunan Kwankwasiyya, wanda hakan ke nuna sunyi hannun riga da tsarin tsohon gwamnan jihar Kano kuma madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Siyasar Kano: Anyi bikin kona Jar hular Kwankwasiyya a Kano (Hotuna)

Anyi bikin kona Jar hular Kwankwasiyya a Kano

Ruwa dai yayi tsami tsakanin gwamna Ganduje da tsohon maigidansa Kwankwaso jim kadan bayan kammala zabukan 2015, sai dai rikicin nasu yayi kamari ne a lokacin da Sanata Kwankwaso ya kai ziyarar ta’aziya lokacin d mahaifiyar Ganduje ta rasu, inda ya samu tarba daga dubun dubatan jama’a.

Siyasar Kano: Anyi bikin kona Jar hular Kwankwasiyya a Kano (Hotuna)

Kona jar hula

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yayin da ake rikicin siasar Kano, shiko Sarkin Kanon caccakar shuwagabannin Arewa yayi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel