Tashin hankali: An sace wani Kwamishinan wata Jiha

Tashin hankali: An sace wani Kwamishinan wata Jiha

– ‘Yan bindiga sun sace wani Kwamishina a Jihar Kuros Riba

– Yanzu haka an yi garkuwa da Gabriel Odu-Orji

– Wannan abu dai ya faru ne jiya Lahadi

Tashin hankali: An sace wani Kwamishinan wata Jiha

Gwamnan Jihar Kuros-Riba Ayade

Rahotanni na zuwa mana nan NAIJ.com cewa an sace wani Kwamishinan Jihar Kuros-Riba. Wadanda abin ya faru a gaban su jiya suna cewa wasu ‘yan bindiga ne su 5 suka jefa sa cikin wata mota da kusan azahar.

James Ibri wanda aka yi a gaban idanun sa ya bayyanawa Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN yadda abin ya wakana. Yace sun zo ne a wata tsanwar mota kirar Audi nan su ka yi gaba da Kwamishinan a katuwar motar sa.

KU KARANTA: Ba zan bar APC ba Inji Gwamnan Adamawa

Tashin hankali: An sace wani Kwamishinan wata Jiha

Kwamishinonin Jihar Kuros-Riba

An dai sace Kwamishinan ruwan ne a Unguwar Mayne da ke karamar hukumar Kalaba yayin da ya je cin abinci. Jami’an ‘Yan Sanda dai sun tabbatar da wannan su kace suna bakin aiki iya gwargwado.

Jiya ne kuma Reno Omokri wanda ya zama mai ba tsohon shugaban Jonathan shawara kan hanyoyin sadarwa na zamani yayi kira da cewa Gwmnoni su yi maza-maza su tunbuke AbdulAziz Yari na Jihar Zamfara daga matsayin shugaban su bisa kalaman da ya furta kwanaki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Darasi daga yakin basasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel