Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta karyata furucin gwamnan Jihar Ribas

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta karyata furucin gwamnan Jihar Ribas

- Hedikwatar ‘yan sandan Najeriya ta maida martani bisa zargin da gwamna Wike ya yi cewa sufeto janar na ‘yan sanda ya baiwa kwamishinan ‘yan sandan jihar umarnin ya halaka shi

- Rundunar ‘yan sandan ta ce yanzu dai kimanin jami’an ‘yan sanda 221 ke tsaron lafiyar gwamnan

- Kakakin rundunar ya ce gwamnan bai taba korafin cewa jami’an ‘yan sandan na sakaci ko ganganci da aikin tsaron lafiyarsa ba

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta karyata furucin gwamnan Jihar Ribas

Gwamnan Jihar Ribas Barista Nyesom Wike a lokacin da ya ke ziyarar wasu ayyukan gwamnatin a jihar

Hedikwatar ‘yan sandan Najeriya ta karyata zargin da gwamnan jihar Ribas Barista Nyesom Wike ya yi na cewa sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya halaka gwamnan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Jimoh Moshood, yace wannan abin bakin ciki ne ganin yadda irin wannan magana ke fitowa daga bakin gwamna da kansa. Ya ci gaba da cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya tana sanar da cewa maganar da mai girma gwamna Nyesom Wike ya yi ba gaskiya ba ce. NAIJ.COM ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram sun farma matafiya a Borno

A cewar rundunar ‘yan sandan, yanzu haka kimanin jami’an ‘yan sanda 221 ke tsaron lafiyar mai girma gwamnan, kuma bai taba korafin cewa jami’an ‘yan sandan na sakaci ko ganganci da aikin tsaron lafiyarsa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda 'yan Najeriya ke zanga-zanga rashin amincewa da kyamar baki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel