Jawabin banki ya tabbatar da cewa Fasto Suleman ya aika kudade da dama zuwa asusun Stephanie Otobo

Jawabin banki ya tabbatar da cewa Fasto Suleman ya aika kudade da dama zuwa asusun Stephanie Otobo

- Stephanie Otobo ta saki sabon hujja kan babban fasto Suleman

- Wannan karon, Otobo ta saki jawabin asusun ta na banki ne, Wanda ke nuni ga kudaden da Suleman ya tura mata

- Kamfanin waya dake kasar Canada ma sun yarda zasu saki jawabin kiranta

Jawabin banki ya tabbatar da cewa Fasto Suleman ya aika kudade da dama zuwa asusun Stephanie Otobo

Stephanie Otobo ta saki jawabin banki Fasto Suleman ya aika kudade da dama zuwa asusun ta

Rikici na dada billowa ga shugaban cocin Omega Fire Ministry, fasto Johnson Suleman, yayinda wacce ake zargin abokiyar holewar sa ce ta saki jawabin asusun ta na banki.

KU KARANTA KUMA: Duk dan majalisar da ya yi yunkurin tsige Buhari a bakacin kujerarsa - Inji Kwankwaso

A cikin wani bidiyo da NAIJ.com ta samu, an gano Otobo na nuna ma mutane biyu jawabin asusunta na bankin UBA wanda ke nuna bayani a kan kudaden da fasto Suleman ya aika mata a kai a kai.

A cikin jawabin na asusun, an rahoto cewa fasto Suleman ya aika mata da kudi naira miliyan 1 zuwa asusun ta a ranar 22 ga watan Yuli na shekarar 2015.

Jawabin banki ya tabbatar da cewa Fasto Suleman ya aika kudade da dama zuwa asusun Stephanie Otobo

Jawabin banki ya tabbatar da cewa Fasto Suleman ya aika kudade da dama zuwa asusun Stephanie Otobo

A cikin wata hira da akayi kwanan nan a Toroto, Canada Otobo ta ce fasto Suleman ya daskarar da sabon asusun bankin ta inda yake zaton asusun ta na baya ne wanda a ciki ake zargin ya aika mata da kudi lokuta da dama.

Cikakken bidiyon hira da akayi da Stephanie Otobo a Canada.

Kamfanin wayan da Otobo ke amfani da shi a kasar Canada sun yi alkawarin sakin bayanin kiran da tayi wanda tayi alkawarin nuna sau nawa fasto din ya kira ta lokacin da take Canada.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel