Duk dan majalisar da ya yi yunkurin tsige Buhari a bakacin kujerarsa - Inji Kwankwaso

Duk dan majalisar da ya yi yunkurin tsige Buhari a bakacin kujerarsa - Inji Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan tsaro kuma sanatan Kano ta tsakiya a yanzu, Sanata Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso yace duk dan majalisa da yake gani wuyansa ya isa yanka ya yi kuskuren kawo kudirin tsige shugaba Buhari, to zai tabbatar da cewa ya debo wutar gasa kansa.

Duk dan majalisar da ya yi yunkurin tsige Buhari a bakacin kujerarsa - Inji Kwankwaso

Kwankwaso ya ce duk dan majalisar da ya yi yunkurin tsige Buhari a bakacin kujerarsa

Kwankwaso yace "muna da labarin akwai daga cikin 'yan majalisar wakilai wasu 'yan siyasa dake majalisa masu shirin kawo kudirin tsige shugaban kasa, to ina mai tabbatar masu da cewar kafin su tsige shugaban kasa to mune za mu yi maganinsu, kuma za su gane kurensu."

KU KARANTA KUMA: Boko Haram sun farma matafiya a Borno

Kwankwaso ya kara da cewa "ba za mu bar wasu tsiraru gurbatattu su tuge mana bishiyar mu ba, wacce muka dasa da hannun mu, kuma muna mata bayi harsai ta haihu kuma muna kyautata zaton duk dan Najeriya sai ya ci 'ya'yan wannan bishiyar".

NAIJ.com ta samu labarin cewa, Sanata Kwankwaso ya shaida hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata a fadar shugaban kasa a gaban gungun 'yan jaridu bayan ganawar su da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon ministan tsaron, ya kara da cewar har yanzu yana kyautata zaton shugaban kasa Buhari zai fitar da kasar daga halin da jam'iyyar PDP ta jefa ta.

Tsohon gwamnan ya kuma roki 'yan Najeriya musamman 'yan jam'iyyar su ta APC mai mulki da su cigaba da marawa shugaban kasar baya da jam'iyayr APC don ganin sun yi nasara.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Sojoji, yan sanda sun yaki yan bindiga, an kashe jami’an tsaro 7

Kana Kwankwaso ya roki 'yan kasar da su ci gaba da addu'o'in samun cikekken lafiya ga shugaban kasar don ganin ya yi nasara.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Wani mutumi ya lashi takobin yin sata idan abubuwa basu daidaita ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel