Tofa: An nemi a tsige Gwamna Yari

Tofa: An nemi a tsige Gwamna Yari

– An yi kira da a sauke Gwamna Yari na Zamfara

– Gwamna Yari yayi wasu kalamai game da annobar sankarau kwanaki

– Da dama sun soki kalaman Gwamnan su kace da sake

Tofa: An nemi a tsige Gwamna Yari

Cutar Sankarau: A tsige Yari Inji Omokri

Reno Omokri wanda ya zama mai ba tsohon shugaban Jonathan shawara kan hanyoyin sadarwa na zamani yayi kira da cewa Gwamnoni su yi maza-maza su tunbuke AbdulAziz Yari na Jihar Zamfara daga matsayin shugaban su bisa kalaman da ya furta kwanaki.

Gwamna Yari ya bayyana cewa zunuban jama’a na cikin abin da ya jawo cutar sankarau da aka rasa gane kan ta. Cutar na cigaba da zagaye Jihohin kasar nan. Da dama dai sun mutu a Sokoto, Bauchi, Katsina, Zamfara da ma wasu Garuruwan a halin yanzu.

KU KARANTA: An samu barkewar sankarau a Jihar Adamawa

Tofa: An nemi a tsige Gwamna Yari

Cutar sankarau na cigaba da yi wa mutane illa

Omokri yace karya ake yi ace babu maganin irin wannan nau’i na sankarau, yace bari ma tun kusan shekaru 10 da su ka wuce Majalisar dinkin Duniya ta gano maganin kuma har wasu sun warke. Mista Omokri yayi tir da wannan kalamai da Gwamnan APC yace ba haka tsohon shugbaa Jonathan yayi ba a lokacin da Ebola ta barke a kasar, cewar NAIJ.com.

Ko kwanakin baya dai Sarkin Kano Sanusi II yayi kaca-kaca da kalaman da Gwamnan Zamfara ya furta na cewa Ubangiji ne ya kawo sankarau. Jama’a dai su kace shugabannin sun gagara yin komai.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Har yanzu ana fafutukar gano 'Yan matan Chibok

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel