Bukola Saraki yayi magana game da shugaban kasa; Ka ji abin da ya fada

Bukola Saraki yayi magana game da shugaban kasa; Ka ji abin da ya fada

– A wata hira da Jaridar Daily Trust tayi da Saraki ya bayyana abubuwa da dama

– Shugaban Majalisar datttawar yace yana bayan shugaban kasa Buhari

– Sannan Bukola Saraki yace bai karkatar da kudin Jihar Kwara ba

Bukola Saraki yayi magana game da shugaban kasa; Ka ji abin da ya fada

Bukola Saraki da shugaba Buhari

Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewa yana bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari dari-bisa-dari. Saraki ya bayyana wannan ne a wata hira da yayi da Daily Trust.

Ko da hirar ba ta fito ba sai gobe, NAIJ.com ta samu tsokaci daga tattaunawar inda shugaban Sanatocin kasar yayi magana game da shugaban kasa Buhari da kuma Ibrahim Magu na Hukumar EFCC.

KU KARANTA: EFCC tayi wani wawan kamu a Legas

Bukola Saraki yayi magana game da shugaban kasa; Ka ji abin da ya fada

Bukola Saraki yace yana tare da shugaban kasa Buhari

Bukola Saraki ya kuma tabbatar da cewa bai karkatar da kudin Jihar Kwara ba kamar yadda ake riyawa. Saraki yake cewa babu hannun sa a cikin wannan bashi da aka maidowa Jihohi na Paris Club.

A karshen tikewa dai Sanata mai wakiltar gabashin Kogi Dino Melaye ya karbi takardun shaidar karatun sa na Digirin farko a Jami’ar Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya bayan an ta ce-ce-ku-ce a shekaran jiya Jumu’a da rana kamar yadda mu ka kawo maku rahoto.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kusan duk 'Yan Siyasar Najeriya barayi ne?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel