Yadda Sanata Dino Melaye ya karbi Satifiket din sa

Yadda Sanata Dino Melaye ya karbi Satifiket din sa

– A Ranar Juma’a Dino Melaye ya karbi takardar shaidar karatun sa a Makarantar sa

– An hurowa Sanatan wuta cewa bai kammala Jami’ar ba

– Sai dai shugaban Jami’ar ya wanke Sanatan daga baya

Yadda Sanata Dino Melaye ya karbi Satifiket din sa

Sanata Dino Melaye a ABU Zaria

A karshen tikewa dai Sanata mai wakiltar yammacin Jihar Kogi Dino Melaye ya karbi takardun shaidar karatun sa na Digirin farko a Jami’ar Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya bayan an ta ce-ce-ku-ce a shekaran jiya Juma’a da rana.

An tasa Sanatan a gaba inda aka ce bai kammala karatun sa ba, sai dai shugaban Jami’ar ta A.B.U Farfesa Ibrahim Garba ya wanke sa a gaban kwamitin Majalisar. Bayan nan ne Sanatan yace zai karbi satifiket din na sa wanda bai karba ba tun tuni idan ya zo darasi makon gaba don kuwa yanzu yana karatun wani Digiri na uku a Jami’ar.

KU KARANTA: Ana cacar baki tsakanin Majalisa da wani Gwamna

Dino Melaye bai samu zuwa ba wancan makon saboda ana hutun rabin zango a Jami’ar. Sai wannan mako ne ya samu karbar takardun na sa. NAIJ.com ta zagaya har gaban ofishin Jami’ar na Senate inda matasa su ka yi cincirindo suna jiran gwanin na su.

Dino Melaye ya karbi takardar sa ya kuma zagaya ya ga shugabannin Jami’ar irin su Rajistra Mal. A.A Kundila. A karshe dai ya karbi takardar satifiket din sa inda yace ‘yan bakin ciki sun sha kunya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Masu rubuta JAMB sun koka wannan shekara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel