Saudiya za ta gina birnin nishadi a kusa da Riyadh

Saudiya za ta gina birnin nishadi a kusa da Riyadh

Saudiya ta na shirin gina abin da ta bayyana a matsayin birnin nishadi a wajen babban birnin kasar, Riyadh.

Saudiya za ta gina birnin nishadi a kusa da Riyadh
Saudiya za ta gina birnin nishadi a kusa da Riyadh

A shekarar 2022 ake sa ran bude birnin, a inda za a rinka bukukuwan baje kolin al'adu, da wasanni da kuma abubuwan shakatawa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya nada sababbin shugabannin hukumomi da ma’aikatun ma’aikatar Ilimi

Legit.ng ta rahoto cewa mataimakin yarima mai jiran gado a Saudiya, Mohammed bin Salman ya ce ana fatan birnin da za a gina, zai zama wani wuri mai muhimmanci ga raya al'adu da cimma bukatun mutane masu tasowa a kasar a gaba.

Gwamnatin Saudiya na fatan wannan shiri da ake wa lakabi da Vision 2030, zai samar da guraben ayyukan yi ga matasa a kasar, tare da yin sassauci ga wasu tsauraran ka'idoji a kasar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon yadda matasa ke ta murna a lokacin da shugaba Buhari ya dawo Najeriya daga birnin Landan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel