Ministan kuɗi dana kasafin kuɗi sun gurfana gaban majalisar wakilai

Ministan kuɗi dana kasafin kuɗi sun gurfana gaban majalisar wakilai

- Majalisa ta gayyaci ministoci kamar yadda suka amsa kira da kuma yan fansho zasu dara

- Biyo bayan gayyatan da majalisar wakilai ta aika ma ministan kudi da ministan kasafin kudi da tsare tsare da su gurfana gabanta don tsatstsage mata bayanai dangane da kudin fansho, ministocin sun amsa kira

Ministan kuɗi dana kasafin kuɗi sun gurfana gaban majalisar wakilai

Ministocin yayin da suke shigowa majalisa

A jiya Alhamis 6 ga watan Afrilu ne ministan kudi Kemi Adeosun tare da takwaranta na ma’aikatan kasafi da tsare tsare Udoma Udo suka bayyana gaba majalisar suka bada bahasi, shima shugaban yan fansho na kasa Dakta Abel Afolayan ba’a bar shi a baya ba.

KU KARANTA:‘Almajirai miliyan 3 muke dasu a jihar Kano’ – Gwamna Ganduje

Ministan kuɗi dana kasafin kuɗi sun gurfana gaban majalisar wakilai

Ministan kasafin kuɗi

Kamar yadda NAIJ.com ta samu labari, majalisar ta ce ta gayyaci ministar kudi, Kemi Adeosun da kuma ministan kasafin kudi, Senata Udoma Udoma, bayan korafe-korafe da suka samu daga jama'a da dama.

Bayan kammala zaman, shugaban majalisar Yakubu Dogora ya bayyana cewar ba zasu lamince cin kashin da ake yi ma yan fansho ba, kuma zasu hada kai da bangaren zartarwa don ganin an biya dukkanin yan fansho hakkokinsu.

Ministan kuɗi dana kasafin kuɗi sun gurfana gaban majalisar wakilai

Ministan kuɗi yayin da take jawabi

Dogara ya cigaba da fadin: “Lokacin da shugaban kasa yayi alkawarin biyan yan fansho,sai gashi abin kamar wasa, an sakar musu kudadensu duk da halin karayar tattalin arzikin da ake ciki, kuma ina fatar wannan shine karo na karshe da zamu kara sa baki kan lamarin yan fansho.”

Ministocin sun samu rakiyar shugaban hukumar dake kula da yan fansho, uwargida Sharon Ikeazor.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wai shin ko dai a rusa majalisa ne?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel