Janar Bamaiyi ya cirewa Osinbajo zani a kasuwa

Janar Bamaiyi ya cirewa Osinbajo zani a kasuwa

– Janar Bamaiyi ya fallasa mataimakin shugaban kasa Osinbajo

– Bamaiyi yana cigaba da fallasa abubuwan da ya faru a baya

– Ishaya Bamaiyi yace Osinbajo yayi kutun-kutun a shari’ar sa

Janar Bamaiyi ya cirewa Osinbajo zani a kasuwa

Janar Ishaya Bamaiyi

Janar Ishaya Bamaiyi yana cigaba da fallasa yadda abubuwa su ka wakana a baya a littafin sa da yake kokarin kare Marigayi Janar Sani Abacha. Yanzu dai abin har ya kai ta kan mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo.

Ishaya Bamaiyi ya bayyana yadda Farfesa Osinbajo a lokacin yana Kwamishinan shari’a na Jihar Legas ya nemi cin hanci a hannun sa. A shekarun baya da suka wuce an yi shari’ar tsohon hafsun Sojin kasar a lakacin Janar Sani Abacha.

KU KARANTA: Kudin Hajji a wannan shekarar

Janar Bamaiyi ya cirewa Osinbajo zani a kasuwa

Karya Janar Bamaiyi yake yi Inji Osinbajo

Janar Bamaiyi da aka zarga da yunkurin kashe Mr. Alex Ibru yace an nemi rashawar Miliyan 10 a lokacin Osinbajo yana Kwamishina a Legas. Sai dai mataimakin shugaban kasar ya karyata wannan magana da bakin mai magana da yawun sa.

Kwanaki Bamaiyi yake cewa su Janar Abdussalami sun san da mutuwar tsohon dan takarar shugaban kasa MKO Abiola wanda yace akwai abin da ya kashe sa kuma Janar Abdussalami kadai zai iya bayani.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An yi zangar-zangar BringBackOurGirls

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel