2019: Fastocin takarar Sule Lamido sun mamaye ofishin PDP

2019: Fastocin takarar Sule Lamido sun mamaye ofishin PDP

- An kada gangan siyasar 2019 da kuma kamar tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido zai yi takara

- Da yiyuwar da jama'an Legas suna goyon bayansa

Fastoci na takarar shugaban kasa da tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya shirya yi sun mamaye sakatariyar PDP reshen jihar Legas a jiya Alhamis 6 ga watan Afrilu.

2019: Fastocin takarar Sule Lamido sun mamaye ofishin PDP

Sule Lamido

Fastocin dake dauke da hotunan Sule Lamido sun watsu ne a jihar, inda aka lillikasu a wurare daban daban cikin sakatariyar jam’iyyar PDP na Legas.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta bukaci da a kashe kudi wajen inganta rayuwar mata

Jaridar Daily Trust ta hangi wasu yayan jam’iyyar sanye da riguna dake dauke da tambarin ‘2019 sai Lamido’.

A baya ma NAIJ.com ta ruwaito ana tsammanin Sule Lamido na sunsunan kujerar shugabancin kasar nan, inda aka jiyo shi yana fadin idan Allah na son ya zama shugaban kasar nan, sai ya zama, babu wanda ya isa ya hana shi.

Sai dai wasu rahotanni na karkashin kasa na bayyana cewar wasu jiga jigan yan Arewa, kuma yayan jam’iyyar PDP amma mazauna Legas ne ke ingiza takarar Lamido.

Daya daga cikinsu mai suna Hassan Mohammed yace: “Munga irin ayyukan da yayi a Jigawa na tsawon shekaru 8, don haka ya isa ya tafiyar da kasar, shi yasa muke son yayi takara a 2019.”

A wani hannun kuma, jam’iyyar PDP ta jihar Legas ta nisanta kanta da wadannan fastoci, inda tace bata goyon bayan wani dan takara a yanzu, kamar yadda Kaakakin ta Taofik Gani ya shaida.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wasu mata sun ce ba lallai su sake zabar Gwamna Ambode na jihar Legas ba

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel