Kawo yanzu mutane marasa aikin yi 25,000 ne suka yi rijista da Gwamnati

Kawo yanzu mutane marasa aikin yi 25,000 ne suka yi rijista da Gwamnati

- Labaran da muke samu kawo yanzu na nuni da cewa akalla mutane 25,000 ne marasa aikin yi da suka samu damar yin rijista da gwamnatin tarayya kawo yanzu bayan fara shirin a ranar Larabar da ta gabata

- Mai karatu dai zi iya tuna cewa gwamnatin tarayya ta fara rijistar marasa aikin yi dake ƙasar nan a wani ɓangare na tattara alƙaluman marasa aikin yi dake ƙasarnan

Minista Ngige

Minista Ngige

NAIJ.com dai ta samu labarin cewa shirin wanda gwamnatin tarayya ta bullo dashi an shirya shi ne a kan yanar gizo-gizo kuma hukumar samar wa da matasa aikin yi ne ta fito da tsarin domin samu bayanai daga wurin marasa aikin yi a fadin kasar nan.

KU KARANTA: Wanzami ya illata wata mata da sunan kaciya

Rijistar dai tayi dai-dai da doka ta uku ta hukumar samar da aiki ta ƙasa NDE wanda doka ya bata dama da ta tattara alƙaluman bayanai na marasa aikin yi da kuma guraben aikin da ake dasu a ƙasarnan a matsayin wata hanya ta haɗa masu neman aiki da kuma ma’aikatu.

A tabakin daraktan yaɗa labarai na hukumar ta NDE Edmund Onwuiri yace dukkanin wasu shirye shiye sun kammala don ganin an ƙaddamar da shirin cikin nasara,inda yace an ware shafin intanet na musamman mai suna www.jobsforall.ngdomin jama’a su shiga suyi rijistar sunayen su.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon kan rayuwar mutane a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel