Madalla! An sake bude matatar mai ta garin Warri

Madalla! An sake bude matatar mai ta garin Warri

Matatar mai mallakar gwamnatin tarayya ta garin Warri dake jihar Delta mai fitar da ganga akalla 125,000 duk rana na fetir, man dizel da kuma kalanzir ta fara aiki gadan-gadan bayan dan gyara da akayi mata.

matatar mai ta garin Warri

matatar mai ta garin Warri

Kamfanin na gwamnatin tarayya mai kula da matatar wato Nigeria National Petroleum Corporation (NNPC) ne dai ya bayyana sanarwar rufe matatar a watan Fabrairun da ya gabata saboda matsalar wutar lantarki da matatar ke fuskanta.

NAIJ.com ta samu labarin cewa wani babban jami'i a ma'aikatar ya bayyana wa manema labarai cewa matsalar na'urar dake samar da wutar lantarkin ce ya jaza dole aka rufe matatar amma yanzu an gyara kuma komai ya cigaba da aiki yadda ya kamata.

KU KARANTA: An saki kudi don biyan fansho ga tsaffin ma'aikata

Haka ma dai jami'in ya bayyana cewa yanzu haka matatar man tana samar da lita miliyan 2.4 ta fetir, lita 2.2 ta kalazar da kuma lita 2.6 ta man dizel a kowace rana ta Allah.

Sauran matatun man dake mallakin gwamnatin tarayya dai sun hada da 2 a garin Fatakwal da kuma 1 a jihar Kaduna kuma duka suna aiki yadda ya kamata.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

To fa! nan kuma wani dan Najeriya ne ke cewaba za zabi Shugaba Buhari ba a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel