Ban yi nadama ba da dakatar dani da Saraki yayi - Ali Ndume

Ban yi nadama ba da dakatar dani da Saraki yayi - Ali Ndume

- Sanata Ali Ndume wanda Majalisar Dattawa ta datakar har na watanni shida ya ce, shi bai yi da na sanin abinda ya yi ba har ya sa aka dakatar da shi.

- Ya fadi hakan ne a Abuja a yayin tattaunawa ta musammma da majiyar mu inda ya kara da cewa, in har akwai wadanda za su yi nadama, sune takwarorinsa wadanda ba su masa adalci ba don korar da suka yi ba tare da wani laifi ba.

Ali Ndume

Ali Ndume

NAIJ.com ta tsinkaye shi yana cewa: "Abinda na yi shine in jawo hankalin akan zarge-zargen da wasu jaridu da 'yan Nijeriya suke wa shugaban Majalisar kan shiga da wasu motoci ba bisa ka'ida ba da Sanata Dino Milaye akan takardun makarantarsa ta bogi ko a yi bincika a gane gsskiyar lamari kuma an yi din, saboda haka ya kamata ne su jinjina mani ba kora ba." In Ndume.

Sanatan ya kara da cewa abin ya zo masa da mamaki matuka ganin ba shine na farko da ya fara irin wannan kira a majalissun biyu wajen ganin an binciki wadanda ake zargi ba amma babu wanda aka taba kora dalilin yin haka sai shi.

KU KARANTA: Najeriya tayi abun burgewa a idon duniya

Da ya ke amsa tambayar majiyar ko yaya ya ke ji game da koran da aka masa tunda tun farko bai zaci hakan zai faru da shi ba.

Ndume yace: "Da hakan ya faru sai kawai na ji in godewa Allah, don shi ya kaddara haka a kaina kuma in ban gode masa ba, lallai na yi butulci don ni, ba kowa ba ne, dan talaka na ke kuma ya fifita ni saboda haka babu hujjar da zan ji zafi don jarabce ni da hakan.

"Ni fa alhamdulillah, shiyasa na bar wa Allah komai duk da wasu da yawa sun san cewa an taka doka wajen koran da aka mani sai dai abinda za su duba, mutanena na mazabata ne suka cutar da su don ni dan aikensu ne amma yau don na ga gaskiya na fadi, sai ga shi ana horar da su."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma yan Najeriya ke fadin ra'ayoyin su game da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras
NAIJ.com
Mailfire view pixel