Nayi nadamar kashe kawuna, laifin shedan ne - Mai laifi

Nayi nadamar kashe kawuna, laifin shedan ne - Mai laifi

- Rundunar yansandan jihar Enugu ta fitar da sanarwar cafke wani mutum mai suna Daniel Ekemezie, da ake zarginsa da kisan kawunsa , Pa Patrick Odoh mai shekaru 83

- Sai dai Dansanda dake magana da yawun rundunar ya bayyana cewa wanda ya aikata kisan ya cije a kan cewa shedan ne ya ba shi shawarar aikata kisan

NAIJ.com ta samu labarin cewa mutumin ya bayyana cewa ranar 4 ga watan March ya je ya dunkulo tsohon har dakinsa tare da daure masa baki da tsumma inda ya kai shi wani daji ya daure shi a gindin bishiya, bayan kwana biyar ya koma ya tarar da shi ya mutu inda ya haka dan rami ya binne shi a nan.

KU KARANTA: Amurka ta kai harin makami mai linzami Syria

Jami'an yansandan sun bayyana cewa wanda ake zargin yana basu hadinkai matuka, wajen kai su duk inda lamarin ya faru, ba tare da bayar da wata wahala ba.

Sannan kuma ya nuna nadamarsa akan akin shedan din da ya aikata.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai wasu jami'an INEC ne a kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel