'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyin su kan shirin farfado da tattalin arziki

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyin su kan shirin farfado da tattalin arziki

‘Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyin su kan wata sabuwar shirin shugaba Muhammadu buhari kan farfado da tattalin arzikin kasa wanda aka kaddamar a ranar Laraba, 5 ga watan Afrilu da ta gabata.

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyin su kan shirin farfado da tattalin arziki

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyin su kan shirin farfado da tattalin arziki

Bayan da shugaba Muhammad Buhari ya kaddamar da sabon shirin farfado da tattalin arzikin kasar, ERGP da zai fara aiki daga wannan shekarar zuwa shekarar 2020, 'yan Najeriya da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta.

'Yan Najeriyar sun bayyana ra'ayoyin nasu ne yayin wani rangadi da ta yi a wasu sassan jihar Oyo dake kudu maso yammacin Najeriya.

Wasu ‘yan Najeriya suka bayyana ra’ayin su da cewa sabon tsarin na da kyau amma akwai bukatar shugaban ya kara mayar da hankali kan hauhawan farashin kayayyaki a kasuwanni. Sai dai mafi yawan lokuta ire-ire wadannan alkawura ba a samun cika wa.

KU KARANTA: Ana neman wani Ministan Buhari da karfi da yaji

Wasu kuma sun mayar da hankali ne a kan yanda 'yan majalisu ke yi wa shugaba Buhari zagon kasa, lamarin da suka ce ya na dagula lissafin shugabancin kasar.

Wasu ‘yan Najeriya kuma sun bayyana wa NAIJ.COM cewa shugaba Buhari na iya kokarin inganta tattalin arzikin Najeriya ta fuskar noma amma kuma akwai bukatar a kara mayar da hankali kan harkar noma.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin magudi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel