Mun saki naira biliyan 54 don biyan kudin yan fansho – Inji Buhari

Mun saki naira biliyan 54 don biyan kudin yan fansho – Inji Buhari

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin tarayyan Najeriya ta saki kudi kimanin naira biliyan 54 don share kudin fansho na tarayya, daga shekarar 2014.

Mun saki naira biliyan 54 don biyan kudin yan fansho – Inji Buhari

Shugaban kasa Buhari ya saki naira biliyan 54 don biyan kudin yan fansho

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ne ya tabbatar da hakan a shafin san a Facebook. Inda ya bayyana cewa a ko da yaushe yana takaicin ganin an jinkirta kudin yan fansho da kuma biyan albashin ma’aikatan gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Ali Modu Sherrif ya fita a fusace yayinda ake ganawa da Jonathan

NAIJ.com ta tattaro cikakken bayanin da Shugaba Buhari ya yi kamar haka: “A ko da yaushe na kan kasance cikin damuwa game da jinkiri da ake samu a wajen biyan albashin ma’aikata da kuma biyan kudin fansho ga ma’aikatan da sukayi ritaya. Kamar yadda na sha fada a baya, duk rayuwar girmana ina kwasan albashi, don haka ina jin radadi da takaici kan lokacin da kowa ke batawa gurin jiran biyan albashi da kudin fansho.

"Wannan ne dalilin da ya sa wannan gwamnati ta jajirce gurin yin duk abunda zata iya don taimakon gwamnatocin jiha, wanda da dama suna fafitika da kudaden su. Tunda muka karbi mulki, na amince da sakin kudade, sake duba ga basusukan gwamnatin jiha, kaddamar da shirin dorewar kasafin kudi ga jihohi, da kuma biyan kudin Paris Club da aka dawo da shi.

"Dukkan wannan na daga cikin kokari da sadaukarwar da muke yi don saukaka rayuwar ma’aikata a fadin kasar, da kuma yawan mutanen da suka dogara a kan su.

"A kokarin cika wannan alkawarin, sannan kuma kamar yadda ministan kudi ta bayyana a farkon wannan mako, yanzun nan muka saki kudi kimanin naira biliyan 54 don share kudin fansho na tarayya, daga shekarar 2014. Don ci gaba zamu tabbatar da cewa bamu bar wata kafa ba da sababbin bashi zasu taru a nan gaba ba.

KU KARANTA KUMA: Hajjin bana: ƙasar Saudiyya ta baiwa Najeriya kujeru 95, 000, jihohi sun samu

"Zan kuma ci gaba da rokon gwamnonin jiha da su dauki biyan albashi da kudin fansho da muhimmanci. Na baku tabbacin cewa gwamnatin tarayya zata ci gaba da baku goyon baya ta dukkan hanyoyin da zamu iya, domin daidaita kudaden ku."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wani mutumi da ya ce zai yi sata idan abunda gwamnati ke so yayi kenan:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel