Ana neman wani Ministan Buhari da karfi da yaji

Ana neman wani Ministan Buhari da karfi da yaji

– Majalisar dokokin Jihar Ekiti na neman Minista Kayode Fayemi

– Ana zargin Fayemi da karkatar da wasu makudan kudi

– Kayode Fayemi yayi gardama ya ki bayyana a gaban ta

Ana neman wani Ministan Buhari da karfi da jiya

Ministan Buhari ya shiga matsala

Majalisar dokokin Jihar Ekiti na neman Ministan ma’adanai na kasa Dr. Kayode Fayemi bisa zargin cewa ya karkatar da wasu makudan kudi a lokacin yana Gwamna. Majalisar ta nemi Fayemi ya bayyana a gaban ta.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari Fayemi ya ki bayyana a gaban Majalisar, asali ma dai ya maka kara ne a Kotu inda yake neman a biya sa Naira 500, sai dai Majalisar tace wannan duk harara ne cikin duhu.

KU KARANTA: Hanyoyin da Buhari zai bi wajen farfado da tattalin kasa

Ana neman wani Ministan Buhari da karfi da jiya

Dr. Fayemi Kayode Ministan Ma'adanai na kasa

Majalisar dai ta nemi Sufeta-Janar na ‘Yan Sanda na kasa ya kawo Ministan kuma tsohon Gwamnan Jihar Dr. Kayode Fayemi da karfi da jiya a gaban ta. Wani Dan Majalisar Sameul Omotoso ya bayyana haka.

Haka shi ma tsohon Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Usman Saidu Nasamu Dakingari ya ga ta kan-sa yayin da Majalisa ta ke neman sa domin yayi mata wasu bayani game da kwangilar jirgin sama da ya bada a lokacin yana ofis.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani Bawan Allah gari yayi masa zafi yace sai yayi sata

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel