Ali Modu Sherrif ya fita a fusace yayinda ake ganawa da Jonathan

Ali Modu Sherrif ya fita a fusace yayinda ake ganawa da Jonathan

-Sherrif ya fita daga taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar PDP

- Yace dalilinsa shine sun raina masa wayo

Ali Modu Sherrif ya fita a fusace yayinda ake ganawa da Jonathan

Ali Modu Sherrif ya fita a fusace yayinda ake ganawa da Jonathan

Rahotannin da jaridar NAIJ.com ke samu yanzu na nuna cewa ganawar da akayi tsakanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Ali Modu Sherrif da Ahmed Makarfi ta kare cikin rikici yayin Ali Modu Sherrif ya fita ya basu waje.

Rikicin jam’iyyar PDP ta canza zani tsakanin Sanata Ahmed Makarfi da Sanata Ali Modu Sherrif.

KU KARANTA: An bankado sabuwar badakala a NNPC

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan yayi kira ga wasu jiga-jigan jam’iyyar domin tattauna yadda za’ayi sulhu. Wadanna jiga-jigan sun kunsh tsohon shugaban majalisan dattawa, Anyim Pious Anyim, da gwamnonin jihar Ekiti da Ribas.

NAIJ.com ta samu cewa Ali Modu Sherrif ya fusata ne saboda ba’a jira shi ba kfin aka fara ganawar ba duk da cewan yayi latti kafin yazo.

Yayinda yake magana da manema labarai bayan ya fita ya basy waje, yace : “Munzo nan ne domin ganawar masu ruwa da tsakin jam’iyyar PDP, kuma jam’iyyar nada shugaba daya wanda shine Ali Modu Sherrif.

“Babu wani ganawar PDP da za’ayi da ba shugaban jam’iyyar ne zai bude taron ba. a yau, nine mutum mafi matsayi a jam’iyyar.”

https://twitter.com/naijcomhausa

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel