Kwamitin fitar da zakkat za ta horar da mata 2000 a kan sana’o’i daban-daban

Kwamitin fitar da zakkat za ta horar da mata 2000 a kan sana’o’i daban-daban

Kwamitin fitar da zakkah ta jihar Sokoto da hadin gwiwar bankin ci gaban musulunci (Islamic Development Bank) za su horar da mata 2000 a jihar Sokoto.

Kwamitin fitar da zakkah ta jihar Sokoto ta ce zai horar da mata 2000 a fadin gundumomi 85 na jihar a kan sana’o’i daban-daban.

Shugaban kwamitin, malam Lawal Maidoki ya yi wannan bayyani a wurin taron bude shirin wanda aka fara a Sokoto a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu da aka fara da mata sama da 500 daga gundumomi 30 a jihar.

Shugaban ya shaida wa NAIJ.COM cewa: "shirin tare da hadin gwiwa Islamic Development Bank ta kudurin yaki da talauci".

"Saboda haka, manufar shirin shine karfafa mata ta amfani da zakka domin rage talauci a tsakani al'umma”.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bada umurnin gina hanyoyi 36 a Najeriya

Kwamishinan harkokin addini na jihar, Alhaji Mani Maishunku ya koka kan yadda barace-bare ke kara yawa a jihar.

Kwamishinan mata da harkokin yara, Hajiya Kulu Sifawa ta yabawa kwamitin kan karfafawa mata a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda sunan Allah ya bayyana a jikin itacen moringa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel