Zakzaky: ‘Yan Shi’a sun yi zanga-zanga a gaban Majalisa

Zakzaky: ‘Yan Shi’a sun yi zanga-zanga a gaban Majalisa

– Dazu ‘Yan Shi’a su ka shirya zanga-zanga a Birnin Tarayya Abuja

– Mabiya Shi’an na kira a saki Malamin su Sheikh Zakzaky

– Wani Dan Majalisar yace za a duba kukan na su

Zakzaky: ‘Yan Shi’a sun yi zanga-zanga a gaban Majalisa

‘Yan Shi’a magoya bayan Zakzaky

NAIJ.com ta samu labari cewa dazu da yamma ne ‘Yan kungiyar IMN ta Shi’a su ka gudanar da zanga-zanga a Birnin Tarayya Abuja a game da babban Malamin su da ake cigaba da daurewa na tsawon lokaci.

Wanda yayi magana a madadin Kungiyar ya bayyana cewa yau fiye da watanni 4 kenan da Alkali Gabriel Kolawale ya bada belin shugaban Shi’an amma har yanzu ba a sake sa ba. Wannan mutumi yayi tir da Gwamnatin kasar.

KU KARANTA: An yi wa wani Dan wasan kwallo sharri

Zakzaky: ‘Yan Shi’a sun yi zanga-zanga a gaban Majalisa

‘Yan Shi’a sun yi zanga-zanga a Majalisa

‘Yan Shi’ar dai sun koka da yadda ake rike masu Malami duk da Kotu tace a sake sa. Fiye da shekara guda kenan da aka kama Sheikh Ibrahim Zakzaky sai dai wani Dan Majalisa Honarabul Alhassan Doguwa yace Majalisa za ta duba lamarin.

Haka kuma dazu mu ke samun labari cewa an kara gurfanar da mai ba da shawara kan harkar tsaro a lokacin shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan a gaban kotun tarrayya na Abuja. Tun ba yau ba dai aka kama Sambo Dasuki bisa wasu manyan laifuffuka.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sarkin Kano Muhammad Sanusi II yayi zazzaga

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel